Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Egypt: Jacob, &c presented to Pharaoh

10 ayoyi · 105 fannoni

Ayoyi game da Jacob, &c presented to Pharaoh

  1. Yusuf ya tafi yă faɗa wa Fir’auna, “Mahaifina da ’yan’uwana, tare da garkunansu da shanunsu da kome da suke da shi, sun zo daga ƙasar Kan’ana, suna kuwa a Goshen yanzu.”

  2. Sai ya zaɓi mutum biyar daga cikin ’yan’uwansa, ya gabatar da su a gaban Fir’auna.

  3. Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?” Suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Bayinka makiyaya ne, kamar yadda kakanninmu suke.”

  4. Suka kuma ce masa, “Mun zo, mu zauna a nan na ɗan lokaci, gama yunwa ta yi tsanani a Kan’ana, dabbobin bayinka kuma ba su da wurin kiwo. Saboda haka yanzu, muna roƙonka, bari bayinka su zauna a Goshen.”

  5. Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Mahaifinka da ’yan’uwanka sun zo maka,

  6. ƙasar Masar kuma tana gabanka, ka zaunar da mahaifinka da ’yan’uwanka a sashe mafi kyau na ƙasar, bari su zauna a Goshen. Idan kuma ka ga waɗansu a cikinsu da suka fi dacewa, sai ka sa su lura mini da shanuna.”

  7. Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci Fir’auna,

  8. sai Fir’auna ya tambaye shi, “Shekarunka nawa da haihuwa?”

  9. Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.”

  10. Sai Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita.