- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 22:10kusan 1451 K.H.
Kada ku haɗa bijimi da jaki su yi noma tare.
- Maimaitawar Shari’a 22:11kusan 1451 K.H.
Kada ku sa rigar ulu da aka gauraye da lilin aka saƙa.
- Maimaitawar Shari’a 22:12kusan 1451 K.H.
Ku yi tuntu a kusurwan huɗu na rigar da kuke sa.
- Maimaitawar Shari’a 22:13kusan 1451 K.H.
In mutum ya auri mace, bayan ya kwana da ita, sa’an nan ya ƙi ta
- Maimaitawar Shari’a 22:14kusan 1451 K.H.
ya kuma zarge ta, ya ba ta mummunan suna, yana cewa, “Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, ban sami tabbaci cewa ita budurwa ba ce,”
- Maimaitawar Shari’a 22:15kusan 1451 K.H.
sai mahaifin yarinyar da mahaifiyarta su kawo shaida cewa ita budurwa ce wa dattawan gari a ƙofar garin.
- Maimaitawar Shari’a 22:16kusan 1451 K.H.
Mahaifin yarinyar zai ce wa dattawa, “Na ba da ’yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta.
- Maimaitawar Shari’a 22:17kusan 1451 K.H.
Yanzu ya zage ta cewa, ‘Ban sami ’yarku budurwa ba.’ Amma ga shaidar budurcin ’yata.” Sa’an nan iyayenta za su shimfiɗa zanen a gaban dattawan garin,
- Maimaitawar Shari’a 22:18kusan 1451 K.H.
dattawan kuwa za su ɗauki mutumin su hukunta shi.
- Maimaitawar Shari’a 22:19kusan 1451 K.H.
Za su ci masa tara shekel azurfa ɗari, su ba mahaifin yarinyar, domin wannan mutum ya ba wa budurwa mutuniyar Isra’ila mummunan suna. Za tă ci gaba da zama matarsa; ba kuwa zai sake ta ba muddin ransa.
- Maimaitawar Shari’a 22:20kusan 1451 K.H.
Amma fa in zarge gaskiya ne, ba a kuwa sami shaidar budurcin yarinyar ba,
- Maimaitawar Shari’a 22:21kusan 1451 K.H.
sai a kawo ta a ƙofar gidan mahaifinta, a can mazan gari za su jajjefe ta da dutse har tă mutu. Ta yi abin kunya a Isra’ila ta wurin lalaci a yayinda take a gidan mahaifinta. Dole ku fid da mugu daga cikinku.
- Maimaitawar Shari’a 22:22kusan 1451 K.H.
In aka kama wani yana kwance da matar wani, dole a kashe dukansu biyu, wato, mutumin da ya kwana da matar da kuma matar. Dole a fid da mugu daga Isra’ila.
- Maimaitawar Shari’a 22:23kusan 1451 K.H.
In mutum ya sadu da budurwa a gari wadda aka yi alkawarin aure, ya kuma kwana da ita
- Maimaitawar Shari’a 22:24kusan 1451 K.H.
sai ku ɗauki su biyu zuwa ƙofar wannan gari, ku jajjefe su da dutse har su mutum, za a kashe yarinyar domin tana a cikin gari ba ta kuwa yi ihu neman taimako ba, za a kashe mutumin domin ya yi lalata da matar wani. Dole ku fi da mugu daga cikinku.
- Maimaitawar Shari’a 22:25kusan 1451 K.H.
Amma in a bayan gari ne mutumin ya sadu da yarinyar da aka yi alkawari aure, ya kuma yi mata fyaɗe, mutumin da ya yi wannan ne kaɗai zai mutu.
- Maimaitawar Shari’a 22:26kusan 1451 K.H.
Kada ku yi wa yarinyar kome, ba tă yi zunubin da ya cancanci mutuwa ba. Wannan batu ya yi kamar da na mutumin da ya fāɗa wa maƙwabcinsa ya kuma kashe shi.
- Maimaitawar Shari’a 22:27kusan 1451 K.H.
Tun da ya same ta a jeji ne, wataƙila yarinyar ta yi kukan neman taimako, amma babu wani da zai cece ta.
- Maimaitawar Shari’a 22:28kusan 1451 K.H.
In mutum ya sadu da yarinyar da ba a yi alkawarin aurenta ba, ya kuma yi mata fyaɗe, aka kuma kama su,
- Maimaitawar Shari’a 22:29kusan 1451 K.H.
sai yă biya mahaifin yarinyar shekel hamsin na azurfa. Dole yă auri yarinyar, gama ya yi lalata da ita. Ba zai taɓa sake ta ba muddin ransa.
- Maimaitawar Shari’a 22:30kusan 1451 K.H.
Kada mutum yă auri matar mahaifinsa, kada yă ƙasƙantar gādon mahaifinsa.
- Maimaitawar Shari’a 23:1kusan 1451 K.H.
Duk wanda aka daƙe, ko yanke gabansa, ba zai shiga taron jama’ar Ubangiji ba.
- Maimaitawar Shari’a 23:2kusan 1451 K.H.
Duk wanda aka haifa ta wurin cikin shege, har tsara ta goma, zuriyarsa ba za su shiga taron jama’ar Ubangiji ba, har zuwa tsara ta goma.
- Maimaitawar Shari’a 23:3kusan 1451 K.H.
Ba mutumin Ammon, ko mutumin Mowab, ko kuwa wani zuriyarsu da zai shiga taron jama’ar Ubangiji, har tsara ta goma.
- Maimaitawar Shari’a 23:4kusan 1451 K.H.
Gama ba su zo sun tarye ku da burodi da ruwa a hanyarku, sa’ad da kuka fito daga Masar ba, sai ma suka yi haya Bala’am ɗan Beyor daga Fetor a Aram-Naharayim yă furta la’ana a kanku.