Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Karɓi wannan kafara saboda mutanenka Isra’ila, wanda ka fansar, ya Ubangiji, kada kuma ka ɗaura wa mutanenka alhakin jinin mutumin nan marar laifi.” Za a kuwa yi kafarar zub da jinin da aka yi.

  2. Ta haka za ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga cikinku, da yake kun yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

  3. Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, sai Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannuwanku kuka kuma kama su a matsayin bayi,

  4. in ka ga wata kyakkyawar mace wadda ta ɗauki hankalinka a cikin bayin, za ka iya aure ta tă zama matarka.

  5. Ka kawo ta gidanka ka sa tă aske kanta, tă yanka kumbanta

  6. tă kuma tuɓe tufafin da ta sa sa’ad da aka kama ta. Bayan ta zauna a gidanka ta kuma yi makokin mahaifinta da mahaifiyarta wata ɗaya cif, sai ka shiga wurinta ka zama mijinta, za tă kuwa zama matarka.

  7. In ba ka jin daɗinta, ka bar tă tafi inda take so. Ba za ka sayar da ita ko ka yi da ita kamar baiwa ba, da yake ka ƙasƙantar da ita.

  8. In mutum yana da mata biyu, yana kuwa ƙaunar ɗaya, ba ya kuma ƙaunar ɗayan, su biyun kuwa suka haifi masa ’ya’ya maza, sai ya zamana cewa ɗan farin ya kasance na wadda ba ya ƙauna,

  9. to, a ranar da zai yi faɗa wane ne a cikin ’ya’yansa zai riƙe gādon da zai bar musu, kada yă sa ɗan matar da yake ƙauna yă zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan matar da ba ya ƙauna, wanda shi ne ɗan farin.

  10. Dole yă yarda cewa ɗan matar da ba ya ƙaunar ne ɗan fari, ta wurin ba shi rabo kashi biyu na dukan abin da yake da shi, gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.

  11. In mutum yana da gagararren ɗa mai tawaye, wanda ba ya biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ba ya kuma jin su sa’ad da suke horonsa,

  12. mahaifinsa da mahaifiyarsa za su kama shi su kawo shi ga dattawa a ƙofar garinsu.

  13. Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.”

  14. Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har yă mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro.

  15. In mutum ya yi laifin da ya isa kisa, aka kuwa rataye shi a itace,

  16. kada ku bar jikinsa a kan itacen yă kwana. Ku tabbata kun binne shi a ranar, domin duk wanda aka rataye a kan itace la’ananne ne ga Allah. Kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo.

  17. In kun ga saniya ko tunkiyar ɗan’uwanku wadda ta ɓace, kada ku ƙyale ta, amma ku tabbata kun komar da ita gare shi.

  18. In ɗan’uwan ba ya zama kusa da ku, ko kuwa ba ku san shi ba, sai ku kai ta gida ku ajiye ta sai ya zo nemanta. Sa’an nan ku ba shi ita.

  19. Ku yi haka in kun sami jakin ɗan’uwanku, ko rigarsa, ko kowane abin da ya ɓace. Kada ku ƙyale shi.

  20. In kuka ga jakin ɗan’uwanku, ko saniyarsa ya fāɗi a kan hanya, kada ku ƙyale shi. Ku taimaka, ku tā da shi.

  21. Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yin haka.

  22. In kuka ga gidan tsuntsu kusa da hanya, ko a kan itace, ko kuma a ƙasa, mahaifiyar tsuntsun kuwa tana kwance a kan ’ya’yanta, ko kuwa a kan ƙwanta, kada ku kama mahaifiyar duk da ’ya’yan.

  23. Za ku iya kwashe ’ya’yan, amma ku tabbata kun bar mahaifiyar tă tafi. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.

  24. Sa’ad da kuka gina sabon gida, ku ja masa dakali kewaye da rufinku don kada ku jawo laifin zub da jini a kan gidanku in wani ya fāɗi daga kan rufin.

  25. Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku; in kuka yi haka, ba abin da kuka shuka ne kaɗai zai ƙazantu ba, amma har da inabinku ma.