- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 20:3kusan 1451 K.H.
Zai ce, “Ku ji, ya Isra’ila, yau kuna gab da kama da abokan gābanku. Kada ku karai, ko ku ji tsoro; kada ku firgita, ko ku yi rawar jiki a gabansu.
- Maimaitawar Shari’a 20:4kusan 1451 K.H.
Gama Ubangiji Allahnku, yana tafe tare da ku, zai yaƙi abokan gābanku dominku, yă ba ku nasara.”
- Maimaitawar Shari’a 20:5kusan 1451 K.H.
Hafsoshi za su ce wa mayaƙa, “Ko akwai wanda ya gina sabon gida bai kuma buɗe shi ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă buɗe shi.
- Maimaitawar Shari’a 20:6kusan 1451 K.H.
Ko akwai wani da ya shuka inabi, bai kuwa fara jin daɗinsa ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă ji daɗinsa.
- Maimaitawar Shari’a 20:7kusan 1451 K.H.
Ko akwai wani da aka yi masa alkawarin mata, bai kuwa aure ta ko ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă aure ta.”
- Maimaitawar Shari’a 20:8kusan 1451 K.H.
Sa’an nan hafsoshin za su ƙara da cewa, “Ko akwai wani da yake tsoro, ko ya karai? Bari yă tafi gida don kada ’yan’uwansa su karai su ma.”
- Maimaitawar Shari’a 20:9kusan 1451 K.H.
Sa’ad da hafsoshin suka gama magana da mayaƙan, sai su naɗa komandodi a kansu.
- Maimaitawar Shari’a 20:10kusan 1451 K.H.
Sa’ad da kuka haura don ku fāɗa wa birni, sai ku fara neman garin da salama.
- Maimaitawar Shari’a 20:11kusan 1451 K.H.
In sun yarda da salamar, suka buɗe ƙofofin garinsu, to, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su kuma yi muku aiki.
- Maimaitawar Shari’a 20:12kusan 1451 K.H.
In kuwa suka ƙi salamar, suka fāɗa muku da yaƙi, sai ku yi wa wannan birni ƙawanya.
- Maimaitawar Shari’a 20:13kusan 1451 K.H.
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba da shi cikin hannunku, sai ku kashe dukan mazan da suke cikinsa da takobi.
- Maimaitawar Shari’a 20:14kusan 1451 K.H.
Game da mata, yara, dabbobi da kuma sauran abubuwan da suke cikin birnin, za ku iya kwasa waɗannan a matsayin ganima wa kanku. Za ku kuma yi amfani da ganimar da Ubangiji Allahnku ya ba ku daga abokan gābanku.
- Maimaitawar Shari’a 20:15kusan 1451 K.H.
Haka za ku yi da dukan biranen da suke nesa da ku, waɗanda kuma ba na al’ummai da suke kusa ba.
- Maimaitawar Shari’a 20:16kusan 1451 K.H.
Amma fa, a cikin biranen al’ummai da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kada ku bar wani abu mai numfashi da rai.
- Maimaitawar Shari’a 20:17kusan 1451 K.H.
Ku hallaka su ƙaƙaf, wato, Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa, yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku.
- Maimaitawar Shari’a 20:18kusan 1451 K.H.
In ba haka ba, za su koya muku ku bi dukan abubuwan banƙyaman da suke yi, ta yin sujada wa allolinsu, ta haka kuwa ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.
- Maimaitawar Shari’a 20:19kusan 1451 K.H.
Sa’ad da kuka yi wa birni ƙawanya kuka daɗe, kuka yi ta yaƙi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari, domin za ku ci ’ya’yansu. Kada ku sassare su. Gama itatuwan da suke cikin gonaki, ba mutane ne da za ku yi musu ƙawanya?
- Maimaitawar Shari’a 20:20kusan 1451 K.H.
Amma fa, za ku iya sassare itatuwan da kuka sani ba sa ba da ’ya’ya, ku kuma yi amfani da su don ayyukan gina ƙawanyar, sai an ci birnin da yaƙi.
- Maimaitawar Shari’a 21:1kusan 1451 K.H.
In aka sami an kashe mutum kwance a fili, a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, ba a kuma san wanda ya kashe shi ba,
- Maimaitawar Shari’a 21:2kusan 1451 K.H.
sai dattawanku da alƙalanku su je su gwada nisan wurin da gawar take zuwa garuruwan da suke maƙwabtaka.
- Maimaitawar Shari’a 21:3kusan 1451 K.H.
Sai dattawan garin da suke kurkusa da gawar su ɗauki karsanar da ba a taɓa yin aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba,
- Maimaitawar Shari’a 21:4kusan 1451 K.H.
a gangara da ita kwarin da ba a taɓa nome, ko shuki a ciki ba, inda kuma akwai rafi mai gudu, a can cikin kwarin za su karye wuyanta.
- Maimaitawar Shari’a 21:5kusan 1451 K.H.
Firistoci, ’ya’yan Lawi maza, za su fito, gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su su yi masa hidima, su kuma furta albarku a cikin sunan Ubangiji, za su kuma daidaita duk rigimar cin mutunci.
- Maimaitawar Shari’a 21:6kusan 1451 K.H.
Sa’an nan dukan dattawan garin da yake kurkusa da gawar za su wanke hannuwansu a bisa karsanan da aka karye wuyar a kwarin,
- Maimaitawar Shari’a 21:7kusan 1451 K.H.
za su kuma furta, “Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga an yi haka ba.