- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 17:16kusan 1451 K.H.
Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.”
- Maimaitawar Shari’a 17:17kusan 1451 K.H.
Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba.
- Maimaitawar Shari’a 17:18kusan 1451 K.H.
Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa.
- Maimaitawar Shari’a 17:19kusan 1451 K.H.
Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali
- Maimaitawar Shari’a 17:20kusan 1451 K.H.
don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.
- Maimaitawar Shari’a 18:1kusan 1451 K.H.
Firistocin da suke Lawiyawa, tabbatacce dukan kabilar Lawi, ba za su sami rabo ko gādo tare da Isra’ila ba. Za su yi rayuwa a kan hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta ne, gama wannan ne gādonsu.
- Maimaitawar Shari’a 18:2kusan 1451 K.H.
Ba za su sami gādo a cikin ’yan’uwansu ba; Ubangiji ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.
- Maimaitawar Shari’a 18:3kusan 1451 K.H.
To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa ta bijimi ne, ko ta tunkiya ce; sai su ba firistoci kafaɗar, kumatun, da kuma kayan cikin.
- Maimaitawar Shari’a 18:4kusan 1451 K.H.
Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku.
- Maimaitawar Shari’a 18:5kusan 1451 K.H.
Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su da zuriyarsu daga cikin dukan kabilanku don su tsaya su yi hidima a cikin sunan Ubangiji har abada.
- Maimaitawar Shari’a 18:6kusan 1451 K.H.
Idan Balawe ya tashi daga wani garinku, wurin da yake da zama a Isra’ila, ya tafi a wurin da Ubangiji ya zaɓa, zai iya dawo a duk lokacin da ya ga dama.
- Maimaitawar Shari’a 18:7kusan 1451 K.H.
Zai iya yin hidima a cikin sunan Ubangiji Allahnsa kamar dukan sauran ’yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke hidima a can, a gaban Ubangiji.
- Maimaitawar Shari’a 18:8kusan 1451 K.H.
Zai sami rabo daidai da sauran, ko da yake ya karɓi kuɗin mallaka na iyali da ya sayar.
- Maimaitawar Shari’a 18:9kusan 1451 K.H.
Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can.
- Maimaitawar Shari’a 18:10kusan 1451 K.H.
Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri,
- Maimaitawar Shari’a 18:11kusan 1451 K.H.
ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.
- Maimaitawar Shari’a 18:12kusan 1451 K.H.
Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku.
- Maimaitawar Shari’a 18:13kusan 1451 K.H.
Dole ku zama marasa zargi a gaban Ubangiji Allahnku.
- Maimaitawar Shari’a 18:14kusan 1451 K.H.
Al’ummai da za ku kora sukan saurari waɗannan masu maita, ko masu duba. Amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.
- Maimaitawar Shari’a 18:15kusan 1451 K.H.
Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamar ni daga cikin ’yan’uwanku. Dole ku saurare shi.
- Maimaitawar Shari’a 18:16kusan 1451 K.H.
Gama abin da kuka nema daga Ubangiji Allahnku ke nan a Horeb, a ranar taro, sa’ad da kuka ce, “Kada ka bari mu ji muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wuta mai girma, in ba haka ba, za mu mutu.”
- Maimaitawar Shari’a 18:17kusan 1451 K.H.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Abin da suka faɗa yana da kyau.
- Maimaitawar Shari’a 18:18kusan 1451 K.H.
Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin ’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi.
- Maimaitawar Shari’a 18:19kusan 1451 K.H.
Duk wanda bai saurari kalmomina da annabin nan yake magana da sunana ba, ni kaina zan nemi hakki a kan mutumin.
- Maimaitawar Shari’a 18:20kusan 1451 K.H.
Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.”