circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Irmiya 39:7kusan 588 K.H.
Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya ya kuma buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babilon.
- Irmiya 39:8kusan 588 K.H.
Sai Babiloniyawa suka cinna wa fadar da kuma gidajen mutane wuta suka farfasa katangar Urushalima.
- Irmiya 39:9kusan 588 K.H.
Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya kwashi mutanen da suka rage a birnin zuwa zaman bauta a Babilon, tare da waɗanda suka riga suka tafi wurinsa, da kuma sauran mutanen.
- Irmiya 39:10kusan 588 K.H.
Amma Nebuzaradan shugaban matsaran ya bar waɗansu matalauta a ƙasar Yahuda, su da ba su da kome; a lokacin kuwa ya ba su gonakin inabi da kuma filaye.
- Irmiya 39:11kusan 588 K.H.
To, fa, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ba da wannan umarnai game da Irmiya ta wurin Nebuzaradan shugaban matsaran sarki cewa,
- Irmiya 39:12kusan 588 K.H.
“Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.”
- Irmiya 39:13kusan 588 K.H.
Saboda haka Nebuzaradan shugaban matsara, Nebushazban babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da sauran hafsoshin sarkin Babilon
- Irmiya 39:14kusan 588 K.H.
suka aika aka kawo Irmiya daga filin matsar. Suka miƙa shi ga Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, don yă kai shi gidansa. Saboda haka ya zauna a can a cikin mutanensa.
- Irmiya 39:15kusan 588 K.H.
Yayinda aka kulle Irmiya a sansanin matsara, maganar Ubangiji ta zo masa cewa,
- Irmiya 39:16kusan 588 K.H.
“Tafi ka faɗa wa Ebed-Melek mutumin Kush, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ina gab da cika maganata a kan wannan birni ta wurin masifa, ba wadata ba. A lokacin za tă cika a idanunka.
- Irmiya 39:17kusan 588 K.H.
Amma zan kuɓutar da kai a wannan rana, in ji Ubangiji; ba zan ba da kai ga waɗanda kake tsoronsu ba.
- Irmiya 39:18kusan 588 K.H.
Zan cece ka; ba za ka mutu ta wurin takobi ba amma za ka tsira da ranka, domin ka dogara gare ni, in ji Ubangiji.’ ”
- Irmiya 40:1kusan 588 K.H.
Sai magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya sake shi a Rama. Ya sami Irmiya a daure da sarƙoƙi a cikin sauran kamammu daga Urushalima da kuma Yahuda waɗanda ake kaiwa zaman bauta a Babilon.
- Irmiya 40:2kusan 588 K.H.
Sa’ad da shugaban matsaran ya sami Irmiya sai ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ya sa wannan masifa saboda wannan wuri.
- Irmiya 40:3kusan 588 K.H.
Yanzu kuma Ubangiji ya cika shi; ya yi kamar yadda ya faɗa. Dukan wannan ya faru domin kun yi zunubi ga Ubangiji ba ku kuwa yi masa biyayya ba.
- Irmiya 40:4kusan 588 K.H.
Amma yau ina ’yantar da kai daga sarƙoƙin da suke a hannuwanka. Zo mu tafi Babilon, in kana so, zan kuwa lura da kai; amma in ba ka so, kada ka zo. Ga shi, dukan ƙasar tana a gabanka; ka tafi duk inda ka so.”
- Irmiya 40:5kusan 588 K.H.
Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi, Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi.
- Irmiya 40:6kusan 588 K.H.
Saboda haka Irmiya ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa ya zauna tare da shi a cikin mutanen da aka bari a ƙasar.
- Irmiya 40:7kusan 588 K.H.
Sa’ad da dukan shugabannin hafsoshin tare da mutanen da suke a karkara suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya ɗan Ahikam gwamna a kan ƙasar ya kuma sa shi ya lura da maza, mata da ’ya’yan da suke mafi talauci a ƙasar da waɗanda ba a kwashe zuwa zaman bauta a Babilon ba,
- Irmiya 40:8kusan 588 K.H.
sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan da Yonatan ’ya’yan Kareya, da Serahiya ɗan Tanhumet maza, ’ya’yan Efai maza, mutumin Netofa, da Yezaniya ɗan mutumin Ma’aka da mutanensu.
- Irmiya 40:9kusan 588 K.H.
Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, ya yi rantsuwa don yă tabbatar musu da mutanensu. Ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Babiloniyawa. Ku zauna a ƙasar ku bauta wa sarkin Babilon, zai kuma yi muku amfani.
- Irmiya 40:10kusan 588 K.H.
Ni kaina zan zauna a Mizfa in zama wakilinku a gaban Babiloniyawa waɗanda za su zo wurinmu, amma ku girbe ruwan inabi, ’ya’yan itatuwa na kaka, da mai, ku zuba su a tulunan ajiyarku, ku kuma zauna a garuruwan da kuka ci.”
- Irmiya 40:11kusan 588 K.H.
Sa’ad da dukan Yahudawan da suke a Mowab, Ammon, Edom da sauran ƙasashe suka ji cewa sarkin Babilon ya bar raguwa a Yahuda ya kuma naɗa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan gwamna a kansu,
- Irmiya 40:12kusan 588 K.H.
sai suka dawo ƙasar Yahuda, wurin Gedaliya a Mizfa, daga dukan ƙasashen da suke a warwatse. Suka girbe ruwan inabi a yalwace da ’ya’yan itatuwan kaka.
- Irmiya 40:13kusan 588 K.H.
Yohanan ɗan Kareya da dukan manyan sojoji da suke a karkara suka zo wurin Gedaliya a Mizfa