Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 37:6kusan 598 K.H.

    Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya annabi cewa,

  2. Irmiya 37:7kusan 598 K.H.

    “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aika a neme ni cewa, ‘Sojojin Fir’aunan da suka fito su taimake ka, za su koma ƙasarsu, Masar.

  3. Irmiya 37:8kusan 598 K.H.

    Sa’an nan Babiloniyawa za su koma su yaƙi wannan birni su ci ta su kuma ƙone shi.’

  4. Irmiya 37:9kusan 598 K.H.

    “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku ruɗe kanku, kuna tsammani, ‘Tabbatacce Babiloniyawa sun bar mu.’ Ba za su bari ba!

  5. Irmiya 37:10kusan 598 K.H.

    Ko da a ce za ku ci dukan sojojin Babiloniyawan da suke yaƙi da ku har raunana ne kawai aka bari a tentunansu, za su fito su ƙone wannan birni.”

  6. Irmiya 37:11kusan 598 K.H.

    Bayan sojojin Babiloniyawa suka janye daga Urushalima saboda sojojin Fir’auna,

  7. Irmiya 37:12kusan 598 K.H.

    sai Irmiya ya bar birnin don yă je yankin Benyamin ya sami rabon mallaka a cikin mutane a can.

  8. Irmiya 37:13kusan 598 K.H.

    Amma sa’ad da ya kai Ƙofar Benyamin, sai hafsa mai tsaro, wanda ake kira Iriya ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama shi ya kuma ce, “Kana gudu daga Babiloniyawa ne!”

  9. Irmiya 37:14kusan 598 K.H.

    Sai Irmiya ya ce, “Ba gaskiya ba ce, ba na gudu daga Babiloniyawa.” Amma Iriya bai saurare shi ba; a maimako, ya kama Irmiya ya kawo shi wurin fadawa.

  10. Irmiya 37:15kusan 598 K.H.

    Suka yi fushi da Irmiya suka sa aka yi masa dūka aka kuma jefa shi cikin kurkuku a gidan Yonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku.

  11. Irmiya 37:16kusan 589 K.H.

    Aka sa Irmiya a can cikin kurkuku, inda ya kasance kwanaki masu yawa.

  12. Irmiya 37:17kusan 589 K.H.

    Sa’an nan Sarki Zedekiya ya aika a kawo shi aka kuma kawo shi fada, inda ya tambaye shi a kaɗaice ya ce, “Akwai wata magana daga Ubangiji?” Irmiya ya amsa ya ce, “I, za a ba da kai ga sarkin Babilon.”

  13. Irmiya 37:18kusan 589 K.H.

    Sai Irmiya ya ce wa Sarki Zedekiya, “Wane laifi na yi maka ko fadawanka ko kuwa wannan mutane, da ka sa aka jefa ni cikin kurkuku?

  14. Irmiya 37:19kusan 589 K.H.

    Ina annabawanka waɗanda suka yi maka annabci suna cewa, ‘Sarkin Babilon ba zai yaƙe ka ko wannan ƙasa ba’?

  15. Irmiya 37:20kusan 589 K.H.

    Amma yanzu, ranka yă daɗe, sarkina, ka saurara. Bari in kawo kukata a gabanka. Kada ka mai da ni gidan Yonatan magatakarda, in ba haka zan mutu a can.”

  16. Irmiya 37:21kusan 589 K.H.

    Sarki Zedekiya ya yi umarni a ajiye Irmiya a sansanin matsara a kuma ba shi burodi daga titin masu gashin burodi kowace rana sai duka burodi a birnin ya ƙare. Saboda haka Irmiya ya zauna a sansanin matsara.

  17. Irmiya 38:1kusan 598 K.H.

    Shefatiya ɗan Mattan, Gedaliya ɗan Fashhur, Yukal ɗan Shelemiya da Fashhur ɗan Malkiya ya ji abin da Irmiya yana faɗa wa dukan mutane sa’ad da ya ce,

  18. Irmiya 38:2kusan 598 K.H.

    “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba, amma duk wanda ya je wurin Babiloniyawa zai rayu. Zai tsira da ransa, ya rayu.’

  19. Irmiya 38:3kusan 598 K.H.

    Kuma ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Tabbatacce za a ba da wannan birni ga sojojin sarkin Babilon, wanda zai ci shi.’ ”

  20. Irmiya 38:4kusan 598 K.H.

    Sai fadawa suka ce wa sarki, “Ya kamata a kashe wannan mutum. Yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran mutane, ta wurin abubuwan da yake faɗa musu. Wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan sai dai wahala.”

  21. Irmiya 38:5kusan 598 K.H.

    “Yana a hannuwanku” Sarki Zedekiya ya amsa. “Sarki ba zai iya yin kome ya hana ku ba.”

  22. Irmiya 38:6kusan 598 K.H.

    Saboda haka suka kama Irmiya suka sa a rijiyar da ba ruwa a ciki ta Malkiya, ɗan sarki, wadda take a sansanin matsara. Suka saukar da Irmiya cikin rijiyar da ba ruwa da igiya; babu ruwa a cikinta, sai laka, Irmiya ya nutse cikin laka.

  23. Irmiya 38:7kusan 598 K.H.

    Amma Ebed-Melek mutumin Kush, wani hafsa a fada, ya ji cewa sun sa Irmiya a rijiyar da ba ruwa. Yayinda sarki yana zama a Ƙofar Benyamin,

  24. Irmiya 38:8kusan 598 K.H.

    Ebed-Melek ya fita daga fadar ya ce masa,

  25. Irmiya 38:9kusan 598 K.H.

    “Ranka yă daɗe sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu a duk abin da suka yi wa Irmiya annabi. Sun jefa shi cikin rijiyar da ba ruwa, inda zai mutu da yunwa gama ba sauran wani burodi a birnin.”