Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 42:5kusan 588 K.H.

    Sa’an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji ya zama shaida na gaskiya da kuma aminci a kanmu in ba mu yi bisa da duk abin da Ubangiji Allahnka ya aike ka ka faɗa mana ba.

  2. Irmiya 42:6kusan 588 K.H.

    Ko ya gamshe mu ko bai gamshe mu ba, za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu, ga wanda muke aikan ka, saboda ya zama mana da amfani, gama za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu.”

  3. Irmiya 42:7kusan 588 K.H.

    Bayan kwana goma sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya.

  4. Irmiya 42:8kusan 588 K.H.

    Saboda haka ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi da dukan jama’a daga ƙarami zuwa babba.

  5. Irmiya 42:9kusan 588 K.H.

    Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni gare shi don in gabatar da kukanku, yana cewa,

  6. Irmiya 42:10kusan 588 K.H.

    ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku.

  7. Irmiya 42:11kusan 588 K.H.

    Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa.

  8. Irmiya 42:12kusan 588 K.H.

    Zan nuna muku jinƙai don yă nuna muku jinƙai ya kuma maido da ku ƙasarku.’

  9. Irmiya 42:13kusan 588 K.H.

    “Amma fa, in kuka ce, ‘Ba za mu zauna a wannan ƙasa ba,’ ta haka kuka kuma nuna rashin biyayya ga Ubangiji Allahnku,

  10. Irmiya 42:14kusan 588 K.H.

    in kuma kuka ce, ‘A’a, za mu tafi mu zauna a Masar, inda ba za mu ga yaƙi ko mu ji ƙarar ƙaho ko mu ji yunwa ba,’

  11. Irmiya 42:15kusan 588 K.H.

    to, ku ji maganar Ubangiji, ya raguwar Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In kun ƙudura ku tafi Masar kuka kuma tafi kun zauna a can,

  12. Irmiya 42:16kusan 588 K.H.

    takobin da kuke tsoro zai same ku a can, kuma yunwar da kuke tsoro za tă bi ku zuwa Masar, a can kuwa za ku mutu.

  13. Irmiya 42:17kusan 588 K.H.

    Tabbatacce, duk waɗanda suka ƙudura suka tafi Masar su zauna a can za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba; ba ko ɗayansu zai tsira ko ya kuɓuta wa masifar da zan aukar a kansu.’

  14. Irmiya 42:18kusan 588 K.H.

    Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama abin la’ana da abin tsoro, abin ƙyama da abin ba’a; ba za ku ƙara ganin wannan wuri ba.’

  15. Irmiya 42:19kusan 588 K.H.

    “Ya ku raguwar Yahuda, Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku je Masar.’ Ku tabbatar da wannan. Na gargaɗe ku yau

  16. Irmiya 42:20kusan 588 K.H.

    cewa in kun yi kuskure sa’ad da kuka aike ni wurin Ubangiji Allahnku kuka kuma ce, ‘Yi mana addu’a ga Ubangiji Allahnmu; ka faɗa mana duk abin da ya faɗa za mu kuwa aikata.’

  17. Irmiya 42:21kusan 588 K.H.

    Na faɗa muku yau, amma har yanzu ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku cikin dukan abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.

  18. Irmiya 42:22kusan 588 K.H.

    Saboda haka yanzu, ku tabbatar da wannan. Za ku mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba a wurin da kuke so ku tafi ku zauna.”

  19. Irmiya 43:1kusan 588 K.H.

    Sa’ad da Irmiya ya gama faɗa wa mutane dukan maganar Ubangiji Allahnsu, duk abin da Ubangiji ya aike shi ya faɗa musu,

  20. Irmiya 43:2kusan 588 K.H.

    Azariya ɗan Hoshahiya da Yohanan ɗan Kareya da dukan masu ɗaga kai suka ce wa Irmiya, “Kana ƙarya ne! Ubangiji Allahnmu bai aike ka ka ce, ‘Kada ku tafi Masar don ku zauna a can.’

  21. Irmiya 43:3kusan 588 K.H.

    Amma Baruk ɗan Neriya yana zuga ka a kanmu don ka ba da mu ga Babiloniyawa, don su kashe mu ko su kai mu zaman bauta a Babilon.”

  22. Irmiya 43:4kusan 588 K.H.

    Saboda haka Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da dukan mutane suka yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da su zauna a ƙasar Yahuda.

  23. Irmiya 43:5kusan 588 K.H.

    A maimako, Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe raguwar Yahuda waɗanda suka dawo su zauna a ƙasar Yahuda daga dukan al’umman inda aka kora su.

  24. Irmiya 43:6kusan 588 K.H.

    Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya.

  25. Irmiya 43:7kusan 588 K.H.

    Saboda haka suka shiga Masar cikin rashin biyayya ga Ubangiji suka tafi har can Tafanes.