Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 44:20kusan 587 K.H.

    Sai Irmiya ya ce wa dukan mutanen, maza da mata, waɗanda suke ba shi amsa,

  2. Irmiya 44:21kusan 587 K.H.

    “Ubangiji bai tuna ya kuma yi tunani game da turaren da aka ƙone a garuruwan Yahuda da kan titunan Urushalima wanda ku da kakanninku, sarakunanku da fadawanku da mutanen ƙasar ba ne?

  3. Irmiya 44:22kusan 587 K.H.

    Sa’ad da Ubangiji bai iya jurewa da mugayen ayyukanku da kuma abubuwa banƙyama da kuka aikata ba, sai ƙasarku ta zama abin la’ana da kufai babu mazauna yadda yake a yau.

  4. Irmiya 44:23kusan 587 K.H.

    Domin kun ƙone turare kuka kuma yi wa Ubangiji zunubi ba ku kuma yi masa biyayya ko ku kiyaye dokarsa ko ƙa’idodinsa ko farillansa ba, wannan masifa ta aukar muku, yadda yanzu kuka gani.”

  5. Irmiya 44:24kusan 587 K.H.

    Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane, har da mata, “Ku saurari maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda a Masar.

  6. Irmiya 44:25kusan 587 K.H.

    Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku!

  7. Irmiya 44:26kusan 587 K.H.

    Amma ku ji maganar Ubangiji, dukan Yahudawan da suke zama a Masar, ‘Na rantse da sunana,’ in ji Ubangiji, ‘cewa babu wani daga Yahuda wanda yake zama a ko’ina a Masar zai ƙara kira bisa sunana ko ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji Mai Iko Duka yana raye.”

  8. Irmiya 44:27kusan 587 K.H.

    Gama ina lura da su don lahani, ba alheri ba; mutanen Yahuda da suke a Masar za su hallaka ta wurin takobi da yunwa sai dukansu sun hallaka.

  9. Irmiya 44:28kusan 587 K.H.

    Waɗanda suka kuɓuta wa takobi suka komo zuwa ƙasar Yahuda daga Masar za su zama kima kawai. Sa’an nan dukan raguwar Yahuda waɗanda suka zo don su yi zama a Masar za su san maganar wane ne za tă tabbata, tawa ko tasu.

  10. Irmiya 44:29kusan 587 K.H.

    “ ‘Wannan zai zama alama a gare ku cewa zan hukunta ku a wannan wuri,’ in ji Ubangiji, ‘saboda ku san cewa barazanata ta lahani a kanku tabbatacce za tă cika.’

  11. Irmiya 44:30kusan 587 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan bayar da Fir’auna Hofra sarkin Masar ga abokan gābansa waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, abokin gāban da ya nemi ransa.’ ”

  12. Irmiya 45:1kusan 607 K.H.

    Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa,

  13. Irmiya 45:2kusan 607 K.H.

    “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk.

  14. Irmiya 45:3kusan 607 K.H.

    Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’ ”

  15. Irmiya 45:4kusan 607 K.H.

    Ubangiji ya ce, “Ka faɗa masa wannan, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan rushe abin da na gina in kuma tumɓuke abin da na dasa, a duk fāɗin ƙasar.

  16. Irmiya 45:5kusan 607 K.H.

    Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’ ”

  17. Irmiya 46:1kusan 607 K.H.

    Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da al’ummai.

  18. Irmiya 46:2kusan 607 K.H.

    Game da Masar. Ga saƙo game da sojojin Fir’auna Neko sarkin Masar, wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ci da yaƙi a Karkemish a Kogin Yuferites a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda.

  19. Irmiya 46:3kusan 607 K.H.

    “Ku shirya garkuwoyinku, manya da ƙanana, ku kuma fito don yaƙi!

  20. Irmiya 46:4kusan 607 K.H.

    Ku shirya dawakai, ku sa musu sirdi! Ku tsaya a wurarenku saye da hulunan kwano a kai! Ku wasa māsunku, ku yafa kayan yaƙinku!

  21. Irmiya 46:5kusan 607 K.H.

    Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, an ci jarumawansu. Suna gudu da sauri ba waiwayawa, akwai razana a kowane gefe,” in ji Ubangiji.

  22. Irmiya 46:6kusan 607 K.H.

    “Masu saurin gudu ba sa iya gudu haka ma masu ƙarfi ba sa iya kuɓuta. A arewa ta Kogin Yuferites sun yi tuntuɓe sun fāɗi.

  23. Irmiya 46:7kusan 607 K.H.

    “Wane ne wannan mai tashi kamar Nilu, kamar koguna masu tafasar ruwaye?

  24. Irmiya 46:8kusan 607 K.H.

    Masar tana tashi kamar Nilu, kamar koguna masu tafasa. Tana cewa, ‘Zan tashi in rufe duniya; zan hallakar da birane da kuma mutanensu.’

  25. Irmiya 46:9kusan 607 K.H.

    Ku yi sukuwar hauka, ya dawakai! Ku tashi a guje, ya mahayan kekunan yaƙi! Ku yi ta fitowa, ya jarumawa, mutanen Kush da kuma Ludim masu riƙon garkuwoyi, mutanen Lidiya, masu iya jan baka.