Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 23:3kusan 715 K.H.

    A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai.

  2. Ishaya 23:4kusan 715 K.H.

    Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku, gama teku ya yi magana ya ce, “Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya; ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.”

  3. Ishaya 23:5kusan 715 K.H.

    Sa’ad da magana ta kai Masar, za su razana da jin labari daga Taya.

  4. Ishaya 23:6kusan 715 K.H.

    Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.

  5. Ishaya 23:7kusan 715 K.H.

    Wannan ce birnin murnanku, birnin nan na tun dā wadda ƙafafunta suka kai ta zama a ƙasashe masu nesa?

  6. Ishaya 23:8kusan 715 K.H.

    Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya ita da take ba da rawanin sarauta, wadda ’yan kasuwanta sarakuna ne, wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?

  7. Ishaya 23:9kusan 715 K.H.

    Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi, don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.

  8. Ishaya 23:10kusan 715 K.H.

    Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu, Ya Diyar Tarshish, gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma.

  9. Ishaya 23:11kusan 715 K.H.

    Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki. Ya ba da umarni game da Funisiya cewa a hallaka kagararta.

  10. Ishaya 23:12kusan 715 K.H.

    Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba, Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya! “Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus; a can ɗin ma ba za ki huta ba.”

  11. Ishaya 23:13kusan 715 K.H.

    Dubi ƙasar Babiloniyawa, wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani! Assuriyawa sun mai da ita wurin zaman halittun hamada; sun gina hasumiyoyin kwanto, suka ragargaza kagararta ƙaf suka mai da ita kango.

  12. Ishaya 23:14kusan 715 K.H.

    Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish; an rurrushe kagararku!

  13. Ishaya 23:15kusan 715 K.H.

    A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,

  14. Ishaya 23:16kusan 715 K.H.

    “Ɗauki garaya, ki ratsa birni, Ya ke karuwar da aka manta da ita; kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa, saboda a tuna da ke.”

  15. Ishaya 23:17kusan 715 K.H.

    A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya.

  16. Ishaya 23:18kusan 715 K.H.

    Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau.

  17. Ishaya 24:1kusan 712 K.H.

    Duba, Ubangiji zai wofinta duniya ya kuma yi kaca-kaca da ita; zai ɓata fuskarta ya watsar da mazaunanta,

  18. Ishaya 24:2kusan 712 K.H.

    zai zama abu ɗaya ga firist kamar yadda yake ga mutane, ga maigida kamar yadda yake ga bawa, ga uwargijiya kamar yadda yake ga baiwa, ga mai sayarwa kamar yadda yake ga mai saya, ga mai karɓan rance kamar yadda yake ga mai ba da rance, ga mai karɓan bashi kamar yadda yake ga mai ba da bashi.

  19. Ishaya 24:3kusan 712 K.H.

    Za a wofinta duniya ƙaƙaf a kuma washe ta sarai. Ubangiji ne ya faɗa haka.

  20. Ishaya 24:4kusan 712 K.H.

    Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane, duniya tana shan azaba ta kuma raunana, masu daraja na duniya suna shan azaba.

  21. Ishaya 24:5kusan 712 K.H.

    Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta sun ƙi yin biyayya da dokoki, sun keta farillai suka kuma karya madawwamin alkawari.

  22. Ishaya 24:6kusan 712 K.H.

    Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya; dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu. Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya, kuma kaɗan ne kurum suka rage.

  23. Ishaya 24:7kusan 712 K.H.

    Sabon ruwan inabi ya bushe kuringar inabi kuma sun yanƙwane; dukan masu farin ciki suna nishi.

  24. Ishaya 24:8kusan 712 K.H.

    Kaɗe-kaɗen garayu sun yi shiru, surutun masu murna ya daina, garayan farin ciki ya yi shiru.

  25. Ishaya 24:9kusan 712 K.H.

    Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa; barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta.