Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Hosiya 10:14kusan 740 K.H.

    hayaniyar yaƙi za tă tashi gāba da mutanenku, saboda a ragargaza kagaranku, kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi, sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da ’ya’yansu da ƙasa.

  2. Hosiya 10:15kusan 740 K.H.

    Haka zai faru da kai, ya Betel, domin muguntarka ta yi yawa. Sa’ad da wannan rana ta zo, za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf.

  3. Hosiya 11:1kusan 740 K.H.

    “Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi, daga Masar kuma na kira ɗana.

  4. Hosiya 11:2kusan 740 K.H.

    Amma yawan kiran da na yi wa Isra’ila haka nesa da ni da suke ta yi. Suka miƙa hadaya ga Ba’al suka kuma ƙona turare ga siffofi.

  5. Hosiya 11:3kusan 740 K.H.

    Ni ne na koya wa Efraim tafiya ina kama su da hannu; amma ba su gane cewa ni ne na warkar da su ba.

  6. Hosiya 11:4kusan 740 K.H.

    Na bishe su da linzamin alheri da tausayi, da ragamar ƙauna; Na cire karkiya daga wuyansu na kuma rusuna na ciyar da su.

  7. Hosiya 11:5kusan 740 K.H.

    “Ba za su koma Masar ba Assuriya kuma ba za tă yi mulki a bisansu ba saboda sun ƙi su tuba ba?

  8. Hosiya 11:6kusan 740 K.H.

    Takuba za su yi ta wulgawa a biranensu, za su hallaka sandunan ƙarafan ƙofofinsu su kuma kawo ƙarshen ƙulle-ƙullensu.

  9. Hosiya 11:7kusan 740 K.H.

    Mutanena sun ƙudura su juye daga gare ni. Ko da ma suka yi kira ga Mafi Ɗaukaka, ta ko ƙaƙa ba zai girmama su ba.

  10. Hosiya 11:8kusan 740 K.H.

    “Yaya zan ba da kai, Efraim? Yaya zan miƙa ka, Isra’ila? Yaya zan yi da kai kamar Adma? Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim? Zuciyata ta canja a cikina; dukan tausayina ya huru.

  11. Hosiya 11:9kusan 740 K.H.

    Ba zan zartar da fushina mai zafi ba, ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba. Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Mai Tsarki a cikinku. Ba zan zo cikin fushi ba.

  12. Hosiya 11:10kusan 740 K.H.

    Za su bi Ubangiji; zai yi ruri kamar zaki. Sa’ad da ya yi ruri, ’ya’yansa za su zo da rawan jiki daga yamma.

  13. Hosiya 11:11kusan 740 K.H.

    Za su zo da rawan jiki kamar tsuntsaye daga Masar, kamar kurciyoyi daga Assuriya. Zan zaunar da su a cikin gidajensu,” in ji Ubangiji.

  14. Hosiya 11:12kusan 740 K.H.

    Mutanen Efraim sun kewaye ni da ƙarairayi, gidan Isra’ila da ruɗu. Mutanen Yahuda kuma suna yi wa Allah ƙin ji, har ma a kan Mai Tsarkin nan mai aminci.

  15. Hosiya 12:1kusan 725 K.H.

    Efraim yana kiwo a kan iska; yana fafarar iskar gabas dukan yini yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici. Ya yi yarjejjeniya da Assuriya ya kuma aika wa Masar man zaitun.

  16. Hosiya 12:2kusan 725 K.H.

    Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda; zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsa zai sāka masa bisa ga ayyukansa.

  17. Hosiya 12:3kusan 725 K.H.

    A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa; a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah.

  18. Hosiya 12:4kusan 725 K.H.

    Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi; ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi. Ya same shi a Betel ya kuma yi magana da shi a can,

  19. Hosiya 12:5kusan 725 K.H.

    Ubangiji Allah Maɗaukaki, Ubangiji ne sunansa sananne!

  20. Hosiya 12:6kusan 725 K.H.

    Amma dole ku koma ga Allahnku; ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya, ku kuma saurari Allahnku kullum.

  21. Hosiya 12:7kusan 725 K.H.

    Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya; yana jin daɗin cuta.

  22. Hosiya 12:8kusan 725 K.H.

    Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”

  23. Hosiya 12:9kusan 725 K.H.

    “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar; zan sa ku sāke zauna a tentuna, kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.

  24. Hosiya 12:10kusan 725 K.H.

    Na yi magana da annabawa, na ba su wahayi da yawa na kuma ba da misalai ta wurinsu.”

  25. Hosiya 12:11kusan 725 K.H.

    Gileyad mugu ne? Mutanensa mutanen banza ne! Suna miƙa bijimai a Gilgal? Bagadansu za su zama tsibin duwatsu. A gonar da aka nome.