Tsallake zuwa abun ciki

Samuel

122 ayoyi · 4 'yan gida

An kuma san shi da: Shemuel

Ayoyin da suka ambaci Samuel

Tace bisa littafi
  1. Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa.

  2. Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.”

  3. Ta haka Isra’ilawa suka ci Filistiyawa. Daga ranan Filistiyawa ba su ƙara yin nasara a kan Isra’ila ba. Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa har ƙarshen zamanin Sama’ila.

  4. Sama’ila kuwa ya ci gaba da mulkin Isra’ila dukan rayuwarsa.

  5. Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.

  6. Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama.

  7. Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji.

  8. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.

  9. Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.

  10. Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.”

  11. Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.

  12. Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.”

  13. Suka haura zuwa birnin, da shigarsu sai ga Sama’ila ya nufo su a hanyarsa ta zuwa kan tudu.

  14. Kafin zuwa Shawulu, Ubangiji ya riga ya bayyana wa Sama’ila ya ce,

  15. Da Sama’ila ya hangi Shawulu, Ubangiji ya ce masa, “Ga mutumin da na yi maka magana, shi ne zai bi da mutanena.”

  16. Shawulu ya sami Sama’ila a hanyar shiga gari, sai ya tambaye shi ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini gidan mai duba?”

  17. Sama’ila ya ce, “Ni ne mai duban, ka yi gaba zuwa ka tudu, gama yau za ka ci tare da ni, da safe kuma in sallame ka, in gaya muku duk abin da yake a zuciyarku.

  18. Sa’an nan Sama’ila ya shiga da Shawulu da baransa ya zaunar da su a gaban waɗanda aka gayyata, mutanen sun kai wajen mutum talatin.

  19. Sama’ila ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman da na ba ka, wannan da na ce ka ajiye dabam.”

  20. Sai mai dahuwan ya ɗauko cinya da abin da yake bisanta ya kawo ya ajiye a gaban Shawulu. Sama’ila ya ce, “Ga abin da aka ajiye dominka. Ka ci, gama an keɓe shi dominka saboda wannan hidima daga lokacin da na ce, ‘Na gayyaci baƙi.’ ” Shawulu kuwa ya ci tare da Sama’ila a ranan nan.

  21. Bayan suka gangaro daga tudu zuwa cikin gari, Sai Sama’ila ya yi magana da Shawulu a ɗakin samansa.

  22. Da asuba sai suka tashi, Sama’ila ya kira Shawulu daga ɗakin sama ya ce, “Ka shirya, zan sallame ka.” Da Shawulu ya shirya, sai Sama’ila da Shawulu suka fita waje tare.

  23. Suna dab da ƙarshen gari, sai Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ka ce wa bawanka yă yi gaba, kai ka ɗan dakata a nan tukuna, domin in ba ka saƙo daga Allah.”

  24. Sai Sama’ila ya ɗauki ’yar kwalabar mai, ya zuba man ɗin wa Shawulu a kansa, ya yi masa sumba yana cewa, “Ubangiji ya keɓe ka shugaba bisa gādonsa.

  25. Da Shawulu ya juya zai bar Sama’ila, sai Allah ya canja wa Shawulu zuciya, alamun nan kuwa suka cika a ranar.