Tsallake zuwa abun ciki

Samuel

122 ayoyi · 4 'yan gida

An kuma san shi da: Shemuel

Ayoyin da suka ambaci Samuel

Tace bisa littafi
  1. A ƙarshe, shi da kansa ya tashi ya tafi Rama. Ya bi ta babban rijiyar ruwan Seku. A can ya yi tambaya ya ce, “Ina Sama’ila da Dawuda suke?” Suka ce, “Suna cikin Nayiwot a Rama.”

  2. Ya tuttuɓe rigunarsa, ya kuma yi annabci a gaban Sama’ila. Ya kwanta tsirara dukan yini da dukan dare. Abin da ya sa ke nan mutane suke cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa ne?”

  3. Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran.

  4. Sama’ila dai ya riga ya rasu, dukan Isra’ila suka yi makokinsa suka binne shi a garinsa a Rama. Shawulu kuma ya kori duk masu duba da masu maitanci daga ƙasar.

  5. Sai matar ta ce, “Wa kake so in hauro maka?” Sai ya ce, “Ki hauro mini da Sama’ila.”

  6. Da matar ta ga Sama’ila sai ta yi ihu da ƙarfi ta ce wa Shawulu, “Me ya sa ka ruɗe ni? Kai ne Shawulu!”

  7. Ya ce, “Yaya kamanninsa yake?” Ta ce, “Wani tsoho sanye da taguwa ne yake haurawa.” Shawulu ya gane cewa Sama’ila ne, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.

  8. Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Don me ka dame ni, ta wurin hauro da ni?” Shawulu ya ce, “Ina cikin babban damuwa ce, Filistiyawa sun fāɗa mini, Allah kuma ya juya mini baya. Bai amsa mini, ko ta mafarki, ko kuma ta annabawa ba, saboda haka na kira ka don ka gaya mini abin yi.”

  9. Sama’ila ya ce, “Don me kake tambayata bayan Ubangiji ya rabu da kai? Ya zama maƙiyinka?

  10. Da jin maganar Sama’ila sai Shawulu ya faɗi ƙasa warwas. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome ba dukan yini da kuma dukan dare.

  11. ’Ya’yan Sama’ila maza su ne, Yowel ɗan fari da Abiya ɗa na biyu.

  12. Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,

  13. Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu. Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci.

  14. Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, suka yi yarjejjeniya da shi a gaban Ubangiji, suka kuwa shafe Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila, yadda Ubangiji ya yi alkawari ta wurin Sama’ila.

  15. Shelomit da ’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe.

  16. Game da ayyukan mulkin Sarki Dawuda, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin Sama’ila mai duba, tarihin annabi Natan da kuma tarihin Gad mai duba,

  17. Ba a taɓa yin Bikin Ƙetarewa haka ba tun zamanin annabi Sama’ila; kuma babu sarkin Isra’ilan da ya taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya yi, tare da firistoci, Lawiyawa da kuma dukan Yahuda da Isra’ila, waɗanda suke can tare da mutanen Urushalima.

  18. Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu.

  19. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi!

  20. “Tabbatacce, dukan annabawa daga Sama’ila zuwa gaba, dukansu da suka yi magana, sun rigya faɗin waɗannan kwanaki.

  21. Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450. “Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Sama’ila.

  22. Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa,