Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda,

  2. zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”

  3. Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.

  4. Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tafi abinsa.

  5. Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina?

  6. Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”

  7. ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,

  8. Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.

  9. Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai

  10. Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.

  11. Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda

  12. rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,

  13. don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,

  14. cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.

  15. ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.

  16. Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.

  17. Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami.

  18. Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron,

  19. A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da mala’ika ya ba shi kafin a yi cikinsa.

  20. Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji

  21. (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”),

  22. An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji.

  23. Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci,

  24. sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa,

  25. “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya.