Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka.

  2. Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.

  3. Saboda haka ko’ina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi.

  4. Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni.

  5. Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa,

  6. Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.

  7. To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,

  8. ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.

  9. Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.

  10. Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata,

  11. an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma.

  12. A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.

  13. Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.

  14. Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Sa’an nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu.

  15. Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye.

  16. Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.

  17. Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu.

  18. Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa,

  19. Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah.

  20. Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah.

  21. Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.

  22. kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.

  23. A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.

  24. Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku.

  25. Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.