Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.

  2. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

  3. Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba.

  4. Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  5. Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

  6. Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu. ’Yan’uwan da suke tare da ni suna gaishe ku.

  7. Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin.

  8. Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,

  9. Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ’yan’uwa cikin Kiristi da suke a Kolossi. Alheri da salama daga Allah Ubanmu, su kasance tare da ku.

  10. Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku.

  11. Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka.

  12. Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu,

  13. Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.

  14. Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah.

  15. Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki

  16. Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna,

  17. wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

  18. Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne.

  19. Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.

  20. Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici.

  21. Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi,

  22. ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.

  23. A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku.

  24. Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.

  25. Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.