Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”

  2. Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu,

  3. a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”

  4. Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?

  5. Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.

  6. Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.

  7. Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,

  8. yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne.

  9. “Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.

  10. Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.

  11. Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.

  12. Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”

  13. Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.

  14. Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”

  15. Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.

  16. In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.

  17. Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

  18. “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.

  19. Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba.

  20. Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.

  21. Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.

  22. Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”

  23. Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.

  24. Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.

  25. Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi.