Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”

  2. Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.

  3. A lokacin nan sarki Hiridus ya ji labarin Yesu,

  4. Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Sa’an nan suka je suka gaya wa Yesu.

  5. Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa.

  6. Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.

  7. Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.”

  8. Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.”

  9. Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.”

  10. Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.”

  11. Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane.

  12. Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron.

  13. Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai,

  14. Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.

  15. Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”

  16. Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”

  17. Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.”

  18. Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu.

  19. Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”

  20. Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”

  21. Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”

  22. Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu

  23. suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

  24. Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce,

  25. “Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”