God
Ayoyin da suka ambaci God
Ka tafi yanzu zuwa ga ’yan’uwanka waɗanda suke zaman bauta ka yi musu magana. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,’ ko ku ji, ko kada ku ji.”
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama, a bayana na ji wata karar babban motsi na cewa, Bari a yabi ɗaukakar Ubangiji a wurin zamansa!
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da ɓacin rai da kuma fushin ruhuna, tare da hannu mai ƙarfi na Ubangiji a bisa na.
A ƙarshen kwana bakwai ɗin maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
“Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro don gidan Isra’ila; saboda haka ka ji maganar da zan yi ka kuma yi musu kashedin nan da ya fito daga gare ni.
In na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ ba ka kuwa yi masa kashedi ko ka tsawata masa a kan mugayen hanyoyinsa don yă ceci ransa ba, wannan mugun zai mutu saboda zunubinsa, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.
“Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.
Hannun Ubangiji ya kasance a kaina a can, ya kuma ce mini, “Tashi ka fita zuwa fili, a can kuwa zan yi maka magana.”
Saboda haka na tashi da tafi fili. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tsaya a can, kamar ɗaukakar da na gani kusa da Kogin Kebar, sai na fāɗi rubda ciki.
Zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka yi shiru ka kuma kāsa tsawata musu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.
Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na ’yan tawaye.
Na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun zunubinsu. Saboda haka cikin kwana 390 za ka ɗauki zunubin gidan Isra’ila.
“Bayan ka gama haka, ka sāke kwantawa, a wannan lokaci a gefen damarka, ka kuma ɗauki zunubin gidan Yahuda. Na ɗora maka kwanaki 40, kwana guda a madadin shekara guda.
Zan ɗaura ka da igiyoyi don kada ka juya daga wannan gefe zuwa wani gefe sai ka gama kwanakin ƙawanyarka.
Ubangiji ya ce, “Ta haka mutanen Isra’ila za su ci ƙazantaccen abinci a cikin al’ummai inda zan kore su in kai.”
Sai na ce, “Ba haka ba ne, Ubangiji Mai Iko Duka! Ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Daga ƙuruciyata har zuwa yanzu ban taɓa cin wani abin da aka samu ya mutu ko abin da namun jeji suka kashe ba. Ba nama marar tsabtan da ya taɓa shiga bakina.”
Sai ya ce, “To da kyau, zan bari ka gasa burodin a kan kashin shanu a maimakon najasar mutane.”
Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, zan yanke tanadin abinci a Urushalima. Mutane za su auna abincin da za su ci da tsoro su kuma auna ruwan da za su sha cikin fargaba,
Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre.
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Urushalima ce wannan, wadda na kafa a tsakiyar al’ummai, da ƙasashe kewaye da ita a ko’ina.
Duk da haka cikin muguntarta ta yi tayarwa a kan dokokina da ƙa’idodina fiye da al’ummai da ƙasashe kewaye da ita. Ta ƙi dokokina ba tă kuwa bi ƙa’idodina ba.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce kin yi ƙin ji fiye da al’umman da suke kewaye da ke ba ki kuma bi ƙa’idodina ko ki kiyaye dokokina ba. Ba ki ma dace da matsayin al’umman da suke kewaye da ke ba.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Ni kaina ina gāba da ke, Urushalima, kuma zan hukunta ki a gaban al’ummai.
Saboda dukan gumakan banƙyamarki, zan yi abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan ƙara yinsa ba.
Saboda haka a cikinki ubanni za su ci ’ya’yansu, ’ya’ya kuma za su ci ubanninsu. Zan hukunta ki zan kuma watsar da dukan waɗanda suke tsira da suke naki a iska.