Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha.

  2. Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.

  3. Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe? Me ya sa ka yashe mu da jimawa?

  4. Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā

  5. sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa.

  6. A shekara ta talatin, a wata na huɗu a rana biyar, yayinda nake cikin ’yan zaman bauta kusa da Kogin Kebar, sai sammai suka buɗe na kuwa ga wahayoyin Allah.

  7. maganar Ubangiji ta zo wa Ezekiyel firist, ɗan Buzi, kusa da Kogin Kebar a ƙasar Babiloniyawa. A can hannun Ubangiji yana a kansa.

  8. Sa’ad da halittun suke tafiya, sai na ji ƙarar fikafikansu, kamar rurin ruwaye masu gudu, kamar muryar Maɗaukaki, kamar hayaniyar rundunar mayaƙa. In sun tsaya cik, sukan sauko da fikafikansu.

  9. Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka hasken da ya kewaye shi. Wannan shi ne kwatancin kamannin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na fāɗi rubda ciki, na kuma ji muryar wani tana magana.

  10. Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.”

  11. Yayinda yake magana, sai Ruhu ya sauko mini ya kuma tā da ni a ƙafafuna, na kuma ji shi yana mini magana.

  12. Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar ’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau.

  13. Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’

  14. Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su ’yan tawaye ne.

  15. Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan ’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.”

  16. wanda ya nannaɗe a gabana. A kowane gefensa akwai rubutun kalmomin makoki da kuka da kuma kaito.

  17. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci abin da yake a gabanka, ka ci wannan littafi; sa’an nan ka tafi ka yi magana wa gidan Isra’ila.”

  18. Saboda haka na buɗe bakina, ya kuma ba ni littafin in ci.

  19. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ci wannan littafin da nake ba ka, ka kuma cika cikinka da shi.” Sai na ci shi, ya kuma yi zaki kamar zuma a bakina.

  20. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka tafi gidan Isra’ila ka faɗa kalmomina gare su.

  21. ba ga mutane da yawa na baƙon harshe da yare mai wuya, waɗanda ba ka san kalmominsu ba. Tabbatacce da na aike ka wurin irinsu, da sun saurare ka.

  22. Amma gidan Isra’ila ba sa niyya su saurare ka domin ba sa niyya su saurare ni, gama dukan gidan Isra’ila sun taurare suna kuma kin ji.

  23. Amma zan sa ka zama mai taurinkai da taurin zuciya kamar su.

  24. Zan sa goshinka ya zama da tauri kamar dutse, da tauri fiye da dutsen ƙanƙara ƙarfi. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.”

  25. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ji da kyau ka kuma lura da dukan kalmomin da nake maka magana.