Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.

  2. Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba,

  3. ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki,

  4. ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?

  5. Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba?

  6. Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?

  7. Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji.

  8. Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce,

  9. “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba.

  10. “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi.

  11. Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka.

  12. Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.

  13. Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.

  14. Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”

  15. Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”

  16. Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.

  17. Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!

  18. Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini

  19. Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi.

  20. Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su.

  21. Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.

  22. Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta.

  23. Ubangiji kansa ya warwatsa su; ya daina duban su. Ba a ba firistoci girma, ba su ba dattawa gata.

  24. Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu, ya fāɗi cikin tarkonsu. Muna tunani cewa za mu iya rayuwa cikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa.

  25. Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki.