God
Ayoyin da suka ambaci God
Adalci ne zai zama abin ɗamararsa aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
Ba za su yi lahani ko su hallaka wani a dutsena mai tsarki ba, gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji kamar yadda ruwaye suka rufe teku.
A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja.
A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa, daga Kush, daga Elam, daga Babiloniya, daga Hamat da kuma daga tsibiran teku.
Zai tā da tuta saboda al’ummai yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila; zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse kusurwoyi huɗu na duniya.
Ubangiji zai busar da bakin tekun Masar; da iska mai zafi zai share hannunsa a bisa Kogin Yuferites Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai saboda mutane su iya hayewa da ƙafa.
Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensa da ta rage daga Assuriya, kamar yadda ta kasance wa Isra’ila sa’ad da suka fito daga Masar.
A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni.
Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”
A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai, a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.
Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa; bari a sanar da wannan ga dukan duniya.
Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”
Na umarci tsarkakana; na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina, waɗanda suke farin ciki a nasarata.
Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu, sai ka ce na babban taron jama’a! Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki, sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa! Ubangiji Maɗaukaki yana shirya mayaƙa don yaƙi.
Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa, daga iyakokin duniya, Ubangiji da kuma fushinsa, zai hallaka dukan ƙasar.
Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki.
Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.
Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa, fiye da zinariyar Ofir wuyan gani.
Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna.
Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su, su da ba su kula da azurfa ba kuma ba sa damuwa da zinariya.
Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.
Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai; zai sāke zaɓi Isra’ila yă kuma zaunar da su a ƙasarsu. Baƙi ma za su zo su zauna tare da su su haɗa kai da gidan Yaƙub.
Al’ummai za su ɗauke su su kuma kawo wurin da yake nasu. Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji. Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.
A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta,