Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Amma mutanen ba su juyo wurin wanda ya buge su ba, balle su nemi Ubangiji Maɗaukaki.

  2. Saboda haka Ubangiji zai yanke Isra’ila kai da wutsiya, da reshen dabino da iwa a rana guda;

  3. Saboda haka Ubangiji ba zai ji daɗin matasa ba, ba kuwa zai ji tausayin marayu da gwauraye ba, gama kowa marar sanin Allah ne da kuma mugu, kowane baki yana faɗin mugayen maganganu. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.

  4. Ta wurin fushin Ubangiji Maɗaukaki ƙasar za tă ci wuta mutane kuma za su zama abin hura wutar, babu wanda zai ji tausayin ɗan’uwansa.

  5. Manasse zai mai da Efraim abinci, Efraim kuma yă cinye Manasse; tare za su yi gāba da Yahuda. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.

  6. don su hana matalauta hakkinsu su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena, suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu suna kuma yi wa marayu ƙwace.

  7. Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammu ko mutuwa cikin waɗanda aka kashe. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.

  8. “Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake!

  9. Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna.

  10. ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”

  11. Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa.

  12. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki, zai aukar da cuta mai kisa a kan ƙosassu jarumawa; a ƙarƙashin sansaninsa zai ƙuna wuta kamar harshen wuta.

  13. Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta, Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta; a rana guda zai ƙone yă kuma cinye ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa.

  14. A wannan rana raguwar Isra’ila, waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub, ba za su ƙara dogara ga wanda ya kusa hallaka su ba amma za su dogara ga Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  15. Raguwa za tă komo, raguwar Yaƙub za su komo ga Maɗaukaki Allah.

  16. Ko da yake mutanenka, ya Isra’ila, sun zama kamar yashin bakin teku, raguwa ce kurum za tă komo. A ƙaddara hallaka, mai mamayewa da mai adalci.

  17. Ubangiji Maɗaukaki, zai sa hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasa ta faru.

  18. Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ya mutanena masu zama a Sihiyona, kada ku ji tsoron Assuriyawa, waɗanda suka dūke ku da sanda suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi.

  19. Ba da daɗewa ba fushina a kanku zai zo ga ƙarshe hasalata kuma za tă koma ga hallakarsu.”

  20. Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya, kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb; zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye, yadda ya yi a Masar.

  21. Duba, Ubangiji Maɗaukaki, zai ragargaza rassa da iko mai girma. Za a sassare itatuwa masu ganyaye, za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa.

  22. Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa; Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko.

  23. Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa, Ruhun hikima da na fahimta, Ruhun shawara da na iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,

  24. zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji. Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba, ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;

  25. amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.