God
Ayoyin da suka ambaci God
Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?
Yanzu zan faɗa muku abin da zan yi da gonar inabina. Zan cire katangar da ta kewaye ta, za tă kuwa lalace; zan rushe bangonta, za a kuwa tattake ta.
Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.”
Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.
Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana, “Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango, za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa.
Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta domin rashin fahimi; manyan mutanensu za su mutu da yunwa talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.
Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya, kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.
waɗanda suke cewa, “Bari Allah yă gaggauta, bari yă hanzarta aikinsa don mu gani. Bari yă iso, bari shirin Mai Tsarkin nan na Isra’ila yă zo, don mu sani.”
Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta, haka saiwarsu za su ruɓa iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura; gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan mutanensa; ya ɗaga hannunsa ya kuma buge su. Duwatsu sun jijjigu, gawawwaki kuwa suka zama kamar juji a tituna. Saboda wannan duka, fushinsa bai huce ba, bai kuwa janye hannunsa ba.
Ya ɗaga tuta don al’ummai masu nisa, ya yi feɗuwa wa waɗanda suke a iyakar duniya. Ga shi sun iso, da sauri da kuma gaggawa!
A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali.
Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.”
Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”
Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?” Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”
Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane, “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba; Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’
Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?” Ya kuma amsa, “Sai an lalatar da biranen ba kowa a ciki, sai an mai da gidaje kangwaye ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,
sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa aka kuma yashe ƙasar gaba ɗaya.
Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki.
Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “ ‘Ba zai faru ba, ba zai auku ba,
Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce,
“Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.”
Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”
Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure?