God
Ayoyin da suka ambaci God
Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.
Ki zo, ya gidan Yaƙub, bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.
Ka rabu da mutanenka, gidan Yaƙub. Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas; suna yin duba kamar Filistiyawa suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.
Ku tafi cikin duwatsu, ku ɓuya cikin ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa!
Za a ƙasƙantar da mai girman kai za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.
Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye domin dukan masu girman kai da masu fariya domin dukan waɗanda aka ɗaukaka (zai kuwa ƙasƙantar da su),
Za a jawo mai girman kai ƙasa a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,
za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.
Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma zuwa tsagaggun duwatsu daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
Yanzu ka duba fa, Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana shirin yă ɗauke kowane tanadi da taimako daga Urushalima da Yahuda dukan tanade-tanaden abinci da kuma dukan tanade-tanaden ruwa,
“Zan sa ’yan yara su zama shugabanninsu; ’yan yara kurum za su yi mulkinsu.”
Amma a ranan nan zai tā da murya ya ce, “Ba ni ba dai. Ba ni da abinci ko abin sawa a gidana; kada ka mai da ni shugaban mutane.”
Urushalima tana tangaɗi, Yahuda yana fāɗuwa; maganganunsu da ayyukansu suna gāba da Ubangiji, suna rena ɗaukakar kasancewarsa.
Matasa suna zalunta mutanena, mata suna mulki a bisansu. Ya mutanena, jagorarinku suna ɓad da ku; suna karkatar da ku daga hanya.
Ubangiji ya ɗauki mazauninsa a cikin ɗakin shari’a; ya tashi don yă shari’anta mutane.
Ubangiji yana shari’a da dattawa da kuma shugabannin mutanensa, “Ku ne kuka lalace gonar inabina; ganimar talakawa suna a gidajenku.
Ina dalilin da kuke marmatsa mutanena kuna gurgurje fuskokin talakawa?” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
Ubangiji ya ce, “Matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya da wuya a miƙe, da idanu masu yaudara, suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali, da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas.
Saboda haka Ubangiji zai kawo gyambuna a kawunan matan Sihiyona; Ubangiji zai sa a aske kawunansu, a bar su ƙwal.”
A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu,
A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila.
Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta.
Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa.
“Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda, ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.