Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah; ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji!

  2. Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa, ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.

  3. Sa’an nan mutane za su ce, “Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai; tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.”

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.

  5. Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.

  6. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela

  7. Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.

  8. Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata,

  9. Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.

  10. Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su.

  11. ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Sela

  12. Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala.

  13. Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata.

  14. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!

  15. Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa.

  16. Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.

  17. Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Sela

  18. Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.

  19. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Da nasara zan rarraba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.

  20. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”

  21. Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

  22. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu.

  23. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.

  24. Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.

  25. Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.