God
Ayoyin da suka ambaci God
Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela
Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.
Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.
Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.
Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.
Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. Sela
Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,
kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.”
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.
Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.
Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.
Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.
Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna; ka tsare raina daga barazanan abokin gāba.
Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi; nan da nan za a buge su su fāɗi.
Dukan mutane za su ji tsoro; za su yi shelar ayyukan Allah su kuma yi tunanin abin da ya aikata.
Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangiji su kuma nemi mafaka a gare shi; bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi!