God
Ayoyin da suka ambaci God
Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.
Na dogara gare ka, ya Ubangiji; za ka amsa, ya Ubangiji Allahna.
Ya Ubangiji, kada ka yashe ni; kada ka yi nesa da ni, ya Allahna.
Zo da sauri ka taimake ni, Ya Ubangiji Mai Cetona.
“Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata da kuma yawan kwanakina; bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.
Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai; yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka. Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum, har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela
“Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema? Begena yana a gare ka.
Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba, gama kai ne wanda ka aikata wannan.
Ka ɗauke bulalarka daga gare ni; na ji jiki ta wurin bugun da hannunka ya yi mini.
Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu; kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi, kowane mutum dai shaƙar iska ne. Sela
“Ka ji addu’ata, ya Ubangiji, ka saurari kukata ta neman taimako; kada ka kurmance ga kukata. Gama ina zama tare da kai kamar baƙo, baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata.
Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji.
Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.
Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna, abubuwan banmamakin da ka aikata. Abubuwan da ka shirya mana. Ba wanda zai iya faɗa maka su; a ce zan yi magana in faɗe su, za su wuce gaban misali a furta.
Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.
Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna; dokar tana cikin zuciyata.”
Na yi shelar adalcinka cikin babban taro; ba na rufe leɓunana, kamar yadda ka sani, ya Ubangiji.
Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata; ina maganar amincinka da cetonka. Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka a gaban taron jama’arka mai girma ba.
Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji; bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji; Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.
Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Ubangiji mai girma ne!”
Ni dai matalauci ne da mai bukata; bari Ubangiji yă tuna da ni. Kai ne taimakona da mai cetona; Ya Allahna, kada ka jinkirta.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.
Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.