God
Ayoyin da suka ambaci God
Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, ka tā da ni, don in sāka musu.
Na sani kana jin daɗina, gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.
Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, har abada abadin.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Maskil ne na ’Ya’yan Kora maza. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah.
Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai. Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne?
Hawayena ne sun zama abincina dare da rana, yayinda mutane suke ce da ni dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?”
Waɗannan abubuwa ne nakan tuna sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina, yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a, ina bishe su a jere zuwa gidan Allah, da sowa ta farin ciki da kuma godiya a cikin taron biki.
Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.
Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.
Zurfi kan kira zurfi cikin rurin matsirgar ruwanka; dukan raƙuma da igiyoyi sun sha kaina.
Da rana Ubangiji yakan nuna ƙaunarsa, da dare waƙarsa tana tare da ni, addu’a ga Allah na raina.
Na ce wa Allah Dutsena, “Me ya sa ka manta da ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba?”
Ƙasusuwana suna jin jiki da wahala yayinda maƙiyana suna mini ba’a, suna ce mini dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?”
Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.
Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah, ka kuma nemi hakkina a kan al’ummai marasa sanin Allah. Ka kuɓutar da ni daga masu ruɗu da mugayen mutane.
Kai ne Allah mafakata. Me ya sa ka ƙi ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba?
Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, bari su bishe ni bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki, zuwa wurin da kake zama.
Sa’an nan zan tafi bagaden Allah, ga Allah, farin cikina da murnata. Zan yabe ka da garaya, Ya Allah, Allahna.
Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da Allahna.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’ya’yan Kora maza. Maskil ne. Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah; kakanninmu sun faɗa mana abin da ka aikata a kwanakinsu, tun dā can.
Da hannunka ka kori al’ummai ka kuma dasa kakanninmu; ka ragargaza mutanen ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka.
Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar, ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba; hannun damanka ne, ƙarfin hannunka, da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.