Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

  2. Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.

  3. Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.

  4. “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.”

  5. Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

  6. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.

  7. Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!

  8. Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela

  9. Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.

  10. Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.

  11. Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi.

  12. Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.

  13. Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.

  14. Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.

  15. Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta.

  16. Yadda muka ji, haka muka gani a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki, a cikin birnin Allahnmu. Allah ya sa ta zauna lafiya har abada. Sela

  17. Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.

  18. Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci.

  19. Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka.

  20. Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.

  21. Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,

  22. Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela

  23. Zabura ta Asaf. Maɗaukaki, Allah, Ubangiji, ya yi magana ya kuma kira duniya daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa.

  24. Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa.

  25. Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi.