Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa.

  2. “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”

  3. Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. Sela

  4. “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku.

  5. Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana.

  6. Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku,

  7. gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai.

  8. Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne.

  9. Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.

  10. Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne?

  11. “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,

  12. ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”

  13. Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?

  14. Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku

  15. Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.

  16. “Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku.

  17. Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”

  18. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina.

  19. Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.

  20. Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki; ka koya mini hikima a wuri can ciki.

  21. Bari in ji farin ciki da murna; bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.

  22. Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina ka kuma shafe dukan kurakuraina.

  23. Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.

  24. Kada ka fid da ni daga gabanka ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.

  25. Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.