Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.

  2. Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa, amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.

  3. Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji.

  4. Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

  5. fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya.

  6. Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu.

  7. Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

  8. Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

  9. Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.

  10. Ta Dawuda. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.

  11. Bari su zama kamar yayi a gaban iska, mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu;

  12. bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi, mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu.

  13. Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangiji in yi kuma murna a cikin cetonsa.

  14. Dukan raina zai ce, “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu, matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”

  15. Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai? Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu, raina mai daraja daga waɗannan zakoki.

  16. Zan yi godiya cikin taro mai girma; cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.

  17. Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji.

  18. Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni! Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana.

  19. Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka, Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina.

  20. Bari waɗanda suke murna saboda nasarata su yi sowa don farin ciki da murna; bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji, wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.”

  21. Harshena zai yi zancen adalcinka da kuma yabonka dukan yini.

  22. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa.

  23. Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai.

  24. Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.

  25. Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.