Yoshuwa 19:6-30
6
Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.
7
Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,
8
da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu.
9
Daga cikin gādon mutanen Yahuda ne aka fitar da gādon kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu, domin rabon da kabilar Yahuda suka samu ya fi ƙarfin abin da suke bukata. Saboda haka kabilar gādon Simeyon yana cikin harabar Yahuda.
10
Ƙuri’a ta uku ta fāɗa a kan Zebulun bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kai har Sarid.
11
Ta nufi yamma zuwa Marala, ta taɓa Dabbeshet, ta wuce zuwa rafin da yake kusa da Yokneyam.
12
Daga Sarid, ta juya gabas zuwa harabar Kislot Tabor, ta kuma wuce zuwa Daberat har zuwa Yafiya.
13
Sa’an nan ta ci gaba, ta yi gabas zuwa Gat-Hefer da Et Kazin; ta ɓulla a Rimmon, ta juya zuwa Neya.
14
A can ne iyakar ta kewaya zuwa Hannaton, sa’an nan ta ƙarasa a Kwarin Ifta El.
15
Zebulun ta ƙunshi garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu. Garuruwan sun haɗa da Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem.
16
Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Zebulun ta samu, bisa ga iyalansu.
17
Ƙuri’a ta huɗu ta fāɗa a kan kabilar Issakar, bisa ga iyalansu.
18
Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Yezireyel, Kessulot, Shunem,
19
Hafarayim, Anaharat,
20
Rabbat, Kishiyon, Ebez,
21
Remet, En Gannim, En Hadda da Bet-Fazez.
22
Iyakar ta taɓa Tabor Shahazuma da Bet-Shemesh ta kuma ƙarasa a Urdun. Duka-duka garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.
23
Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Issakar ta samu, bisa ga iyalansu.
24
Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu.
25
Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Helkat, Hali, Beten, Akshaf,
26
Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat.
27
Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu,
28
ta kai Abdon, Rehob, Hammon da Kana, har zuwa Sidon Babba.
29
Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib,
30
Umma, Afek da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings