Yoshuwa 19:1-9
1
Ƙuri’a ta biyu ta fāɗa a kan kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu ta gādo tana cikin yankin Yahuda.
2
Waɗannan su ne wuraren da suka gāda. Beyersheba (ko Sheba), Molada,
3
Hazar Shuwal, Bilha, Ezem,
4
Eltolad, Betul, Horma,
5
Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa,
6
Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.
7
Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,
8
da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu.
9
Daga cikin gādon mutanen Yahuda ne aka fitar da gādon kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu, domin rabon da kabilar Yahuda suka samu ya fi ƙarfin abin da suke bukata. Saboda haka kabilar gādon Simeyon yana cikin harabar Yahuda.
Settings