Skip to content
Yoshuwa 18:21-28

Biranen Biliyaminu

Yoshuwa 18:21-28
21
Waɗannan su ne garuruwan da kabilar Benyamin suke da su na gādo. Yeriko, Bet-Hogla, Emek Keziz,
22
Bet-Araba, Zemarayim, Betel,
23
Awwim, Fara, Ofra,
24
Kefar Ammoni, Ofni da Geba, garuruwa goma sha biyu ke nan da ƙauyukansu.
25
Akwai kuma Gibeyon, Rama, Beyerot,
26
Mizfa Kefira, Moza,
27
Rekem, Irfeyel, Tarala,
28
Zela, Hayelef, birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima), Gibeya da Kiriyat, garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon kabilar Benyamin bisa ga iyalansu.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.