Skip to content
Yoshuwa 18:11-20

Yoshuwa 18:11-20

11
Ƙuri’ar kabilar Benyamin bisa ga iyalansu. Rabonsu ya kama daga ƙasar da take tsakanin kabilar Yahuda da ta Yusuf.
12
Daga gefen arewa, iyakarsu ta kama ne daga Urdun, ta wuce arewa a gangaren Yeriko, ta nufi yamma cikin ƙasar kan tudu, ta fito a jejin Bet-Awen.
13
Daga can ta ƙetare zuwa gangaren Luz a kudu (wato, Betel), ta wuce zuwa Atarot Adda a tudun arewa na kwarin Bet-Horon.
14
Daga tudun da yake fuskantar Bet-Horon a kudu, iyakar ta juya kudu ta gefen yamma ta ɓullo a Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim), birnin Yahuda. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.
15
A gefen kudu kuwa, iyakar ta fara daga ƙauyukan Kiriyat Yeyarim wajen yamma sai ta miƙe zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa.
16
Iyakar ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskantar Kwarin Ben Hinnom, wanda yake arewa da Kwarin Refayim. Ta ci gaba ta gangara ta Kwarin Hinnom ta yi kudu kusa da birnin Yebusiyawa har zuwa En Rogel.
17
Sai ta nausa ta yi wajen arewa, zuwa En Shemesh, ta ci gaba zuwa Gelilot, wanda yake fuskantar hawan Adummim. Daga can ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ruben.
18
Sai ta wuce ta yi arewancin gangaren Bet-Araba, ta wuce har zuwa cikin Araba.
19
Sa’an nan ta wuce zuwa arewancin gangaren Bet-Hogla ta kuma ɓulla a arewancin gaɓar Tekun Gishiri, a bakin Urdun a kudu. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.
20
Urdun shi ne iyaka a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Benyamin suka gāda.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options