Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Vows

136 ayoyi · 38 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A Shekara ta Murna ɗin, gonar za tă dawo ga mutumin da aka saye ta daga wurinsa, wanda yake mai gonar.

  2. A kimanta kowace daraja bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, gera ashirin ga shekel.

  3. “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare,

  4. “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Bayan kun shiga ƙasar da nake ba ku a matsayin gida,

  5. kuka yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji, daga cikin shanu, ko tumaki, abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa, ko hadayu don alkawura na musamman, ko hadayar yardar rai, ko kuma hadaya ta biki,

  6. sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai.

  7. Da kowane ɗan rago don hadaya ta ƙonawa, a shirya kwalaba ɗaya na ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha.

  8. “ ‘In da rago ne za a miƙa, to, sai a shirya hadaya ta gari mai laushi, garin yă zama kashi biyu bisa goma na efa. A kwaɓa shi da kashi ɗaya bisa uku na garwan mai,

  9. da kashi ɗaya bisa uku na garwan ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. A miƙa ta abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

  10. “ ‘Sa’ad da kuka shirya rago don hadaya ta ƙonawa saboda alkawari na musamman, ko hadaya ta salama ga Ubangiji,

  11. sai ku kawo hadaya ta gari tare da bijimi, kashi ɗaya bisa uku na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da rabin garwan mai.

  12. A kuma kawo rabin garwan ruwan inabi na hadaya ta sha. Za tă zama hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

  13. Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru.

  14. Haka za a yi da kowannensu bisa ga abin da aka shirya.

  15. “ ‘Duk wanda yake ɗan ƙasa, ta haka ne dole zai aikata waɗannan abubuwa sa’ad da ya kawo hadaya da akan yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

  16. Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi.

  17. Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji.

  18. Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’ ”

  19. “Kome a Isra’ila da aka keɓe wa Ubangiji, zai zama naka.

  20. Sai Isra’ila suka yi alkawari wa Ubangiji suka ce, “In ka ba da waɗannan mutane a hannunmu, za mu hallaka dukan garuruwansu ƙaf.”

  21. “ ‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga Ubangiji a lokacin bukukkuwanku, hadayunku na ƙonawa, hadayu na gari, hadayu na sha da hadayu na salama.’ ”

  22. Musa ya ce wa shugabannin kabilan Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.

  23. Sa’ad da mutum ya yi wa Ubangiji alkawari, ko kuwa ya rantse zai yi wani abu, kada yă ƙi cika maganarsa, amma yă cika kome da ya faɗa.

  24. “Sa’ad da yarinya, wadda har yanzu tana a gidan mahaifinta ta yi wa Ubangiji alkawari, ko ta rantse za tă yi wani abu,

  25. mahaifinta kuwa ya ji alkawarin da ta yi, bai kuma ce mata kome ba, to, sai alkawarin da ta yi da wa’adinta su tabbata.