Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Vision

116 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa, “Kada ka ji tsoro, Abram. Ni ne garkuwarka, kuma ladanka zai zama mai girma.”

  2. Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?”

  3. Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.”

  4. Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Wannan mutum ba zai zama magājinka ba, ɗa da yake zuwa daga jikinka ne zai zama magājinka.”

  5. Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.”

  6. Abram ya gaskata, Ubangiji kuma ya lasafta shi adalci ga Abram.

  7. Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.”

  8. Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?”

  9. Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.”

  10. Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba.

  11. Sai tsuntsaye masu cin nama suka sauko a kan gawawwakin, amma Abram ya kore su.

  12. Yayinda rana tana fāɗuwa, sai Abram ya yi barci mai zurfi, sai wani duhu mai kauri mai kuma bantsoro ya rufe shi.

  13. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani tabbatacce cewa shekaru ɗari huɗu, zuriyarka za tă zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, za a mai da su bayi, a kuma wulaƙanta su.

  14. Amma zan hukunta al’ummar da suka yi bauta kamar bayi, daga baya kuma za su fita da mallaka mai yawa.

  15. Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa.

  16. A tsara ta huɗu zuriyarka za tă komo nan, saboda zunubin Amoriyawa bai riga ya cika ba.”

  17. Sa’ad da rana ta fāɗi, aka kuwa yi duhu, sai wata tukunya mai hayaƙi, mai harshen wuta mai ci, ta bayyana, ta kuma wuce tsakanin abubuwan nan da aka tsaga.

  18. suka kuma ga Allah na Isra’ila. A ƙarƙashin ƙafafunsa akwai wani abu wanda aka yi da saffaya, mai haske kuma kamar sararin sama kansa.

  19. Ga Isra’ilawa dai, ɗaukakar Ubangiji ta yi kamar wuta mai ci a kan dutse.

  20. sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa, “Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku, nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi, in yi magana da shi cikin mafarkai.

  21. To, da Yoshuwa ya yi kusa da Yeriko, ya tā da idanunsa ya duba, sai ya ga wani mutum tsaye a gabansa riƙe da takobi, sai Yoshuwa ya je wurinsa ya ce masa, “Kai namu ne ko na abokan gābanmu?”

  22. Mutumin ya ce, “Babu ko ɗaya, na dai zo ne a matsayin shugaban rundunar sojojin Ubangiji.” Sai Yoshuwa ya kwanta da fuskarsa har ƙasa, ya girmama shi, ya ce masa, “Ranka yă daɗe, wane saƙo kake da shi domin bawanka?”

  23. Shugaban rundunar sojojin Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka cire takalmanka, gama wurin da kake tsaye, mai tsarki ne.” Sai Yoshuwa ya cire takalmansa.

  24. Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa.

  25. Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowa yă tafi gida cikin salama.’ ”