Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribe Of Ephraim

46 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?”

  2. Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.”

  3. Bayansa, Abdon ɗan Hillel, daga Firaton, ya shugabanci Isra’ila.

  4. Yana da ’ya’ya maza arba’in da ’yan taɓa kunne talatin, waɗanda suka hau jakuna saba’in. Ya shugabanci Isra’ila shekara takwas.

  5. Sa’an nan Abdon ɗan Hillel ya mutu, aka kuwa binne shi a Firaton a Efraim, a ƙasar tudu ta Amalekawa.

  6. Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.

  7. Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki.

  8. Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.

  9. Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa,

  10. “Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.”

  11. Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “ ‘Ba zai faru ba, ba zai auku ba,

  12. gama kan Aram shi ne Damaskus, kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.

  13. Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’ ”

  14. Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce,

  15. “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.”

  16. Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”

  17. Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure?

  18. Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel.

  19. In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.

  20. Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango.

  21. Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”