Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribe Of Ephraim: Bounds of its inheritance

5 ayoyi · 30 fannoni

Ayoyi game da Bounds of its inheritance

  1. Yankin Efraim ke nan bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kama daga Atarot Addar a gabas zuwa Bet-Horon,

  2. ta wuce zuwa Bahar Rum. Daga Mikmetat a arewa kuwa iyakar ta karkata gabas zuwa Ta’anat Shilo, ta wuce zuwa Yanowa a gabas.

  3. Sai ta gangara daga Yanowa zuwa Atarot da Na’ara, ta bi ta Yeriko, ta kuma fito ta Urdun.

  4. Daga Taffuwa kuma iyakar ta bi yamma zuwa kwazazzaban Kana, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne gādon mutanen Efraim bisa ga iyalansu.

  5. Gādon ya kuma haɗa da dukan garuruwa da ƙauyuka waɗanda aka keɓe wa mutanen Efraim daga cikin gādon mutanen Manasse.