Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribe Of Ephraim: Remonstrated with Gideon for not calling them sooner against Midian
Ayoyi game da Remonstrated with Gideon for not calling them sooner against Midian
To, mutanen Efraim suka ce wa Gideyon, “Me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ba ka kira mu lokacin da ka tafi yaƙi da Midiyawa ba?” Suka zarge shi sosai.
Amma ya ce musu, “Me na yi da za a iya kwatanta da abin da kuka yi? Ashe, kalar inabin da Efraim ta yi bai fi dukan girbin inabin da Abiyezer suka yi ba?
Allah ya ba da Oreb da Zeyib, shugabannin Midiyawa a hannuwanku. Me na yi da ya fi naku? Da ya faɗi haka sai hankalinsu ya kwanta.”