Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribe Of Ephraim: Predictions respecting

5 ayoyi · 30 fannoni

Ayoyi game da Predictions respecting

  1. Game da Yusuf ya ce, “Bari Ubangiji yă albarkaci ƙasarsa da raɓa mai daraja daga sama a bisa da kuma zurfin ruwan da suke kwance a ƙarƙashi;

  2. da abubuwa masu kyau da rana take kawo, da kuma abubuwa mafi kyau da wata zai iya haifar;

  3. da zaɓaɓɓun kyautai na daɗaɗɗun duwatsu, da kyawawan amfani na madawwaman tuddai.

  4. Tare da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta, da tagomashi na wanda yake zama a ƙaramin itace mai ƙonewa. Bari duk waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin sarki a cikin ’yan’uwansa.

  5. Cikin daraja yana yi kamar ɗan fari na bijimi; ƙahoninsa ƙahonin ɓauna ne. Tare da su zai tukwiyi al’ummai, har ma da waɗanda suke ƙarshen duniya. Haka dubu dubban Efraim suke; haka dubban Manasse suke.”