Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Moon

46 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai daraja kamar taurari a jere?

  2. Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba.

  3. Ranarki ba za tă ƙara fāɗuwa ba watanki kuma ba zai ƙara shuɗewa ba; Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.

  4. Yara sukan tara itace, iyaye suka hura wuta, mata kuma sukan kwaɓa kullu don su yi wa Sarauniyar Sama waina. Sukan miƙa hadayun sha ga waɗansu alloli don su tsokane ni in yi fushi.

  5. “ ‘A wancan lokaci, in ji Ubangiji, za a fitar da ƙasusuwan sarakuna da na shugabannin Yahuda, ƙasusuwan firistoci da na annabawa, da kuma ƙasusuwan mutanen Urushalima daga kaburbura.

  6. Za a shimfiɗa su a rana da wata da kuma dukan taurarin sammai, waɗanda suka ƙaunata suka kuma bauta wa, waɗanda suka bi suka nemi shawarar suka kuma yi wa sujada. Ba za a tattara su ko a binne su ba, amma za su zama kamar juji a jibge a ƙasa.

  7. Duk inda na kore su zuwa, dukan waɗanda suka ragu na wannan muguwar al’umma za su gwammaci mutuwa da rai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’

  8. Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya kafa rana don tă yi haske a yini shi da ya sa wata da taurari su yi haske da dare, shi da yake dama teku don raƙuman ruwansa su yi ruri Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

  9. “In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,” in ji Ubangiji, “to, sai zuriyar Isra’ila ta daina zama al’umma a gabana.”

  10. Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa.

  11. Amma tun da muka daina ƙone turare ga Sarauniyar Sama da kuma miƙa mata hadayun sha, muka rasa kome muna ta mutuwa ta wurin takobi da yunwa.”

  12. Matan suka ƙara da cewa, “Sa’ad da muka ƙone turare ga Sarauniyar Sama muka kuma miƙa mata hadayun sha, mazanmu ba su san muna yin waina kamar siffarta muna kuma miƙa mata hadayun sha ba?”

  13. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku!

  14. A gabansu duniya takan girgiza, sararin sama kuma yakan jijjigu, rana da wata su yi duhu, taurari kuma ba sa ba da haske.

  15. Za a duhunta rana da wata, taurari kuma ba za su ba da haske ba.

  16. Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.

  17. “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’

  18. “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.

  19. Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja.

  20. Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini,

  21. Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta.