Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Stones: Memorial pillars of

28 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da Memorial pillars of

Tace bisa littafi
  1. Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa.

  2. Ya kira wannan wuri Betel ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne.

  3. Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa,

  4. har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji zai zama Allahna

  5. kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”

  6. Saboda haka Yaƙub ya ɗauki dutse ya kafa yă zama al’amudi.

  7. Ya ce wa danginsa. “Ku tattara waɗansu duwatsu.” Sai suka kwashe duwatsu suka tsiba, suka kuwa ci abinci a can kusa da tsibin.

  8. Laban ya sa masa suna Yegar Sahaduta, Yaƙub kuwa ya kira shi Galeyed.

  9. Laban ya ce, “Wannan tsibi, shi ne shaida tsakaninka da ni a yau.” Shi ya sa aka kira shi Galeyed.

  10. Aka kuma kira shi Mizfa, domin ya ce, “Ubangiji yă sa ido tsakanin ni da kai sa’ad da muka rabu da juna.

  11. Laban ya ce in ka wulaƙanta ’ya’yana mata, ko ka auri waɗansu mata ban da ’ya’yana mata, ko da yake babu wani da yake tare da mu, ka tuna cewa Allah shi ne shaida tsakaninka da ni.”

  12. Laban ya kuma ce wa Yaƙub, “Ga wannan tsibi, ga kuma wannan al’amudin da na kafa tsakaninka da ni.

  13. Wannan tsibin shi ne shaida, wannan al’amudi kuma shaida ne, cewa ba zan tsallake wannan tsibi zuwa gefenka don in cuce ka ba, kai kuma ba za ka tsallake wannan tsibi da al’amudi zuwa gefena don ka cuce ni ba.

  14. “Ka zaɓi mutum goma sha biyu daga cikin mutane, ɗaya daga kowace kabila,

  15. ka ce musu kowa yă ɗauki dutse ɗaya daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, ku kai su, ku ajiye a inda za ku sauka yau.”

  16. Sai Yoshuwa ya kira mutum goma sha biyu da ya zaɓa daga cikin Isra’ilawa, ɗaya daga kowace kabila

  17. ya ce musu, “Ku je tsakiyar Urdun inda akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku yake. Kowannenku yă ɗauki dutse ɗaya a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilan Isra’ila,

  18. yă zama muku alama. Nan gaba in yaranku suka tambaye ku suka ce, ‘Mece ce ma’anar kasancewar duwatsun nan a nan?’

  19. Sai ku ce musu, ruwan Urdun ya yanke a gaban akwatin alkawari na Ubangiji, a lokacin da akwatin alkawarin ya ƙetare Urdun. Waɗannan duwatsu za su zama abin tuni ga Isra’ilawa har abada.”

  20. Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.

  21. Yoshuwa ya ɗora duwatsu goma sha biyun a tsakiyar Urdun daidai inda firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya. Suna nan a can har wa yau.

  22. Sai Yoshuwa ya kafa duwatsu goma sha biyun nan da suka ɗauko daga Urdun.

  23. Ya ce wa Isra’ilawa, “Nan gaba in yaranku suka tambayi iyayensu suka ce, ‘Mece ce ma’anar waɗannan duwatsun?’

  24. Ku ce musu, ‘Isra’ilawa sun ƙetare kogin Urdun a kan busasshiyar ƙasa.’

  25. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa.