Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Stones: Commandments engraved upon

14 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da Commandments engraved upon

  1. Ubangiji ya ce wa Musa, “Hauro wurina a kan dutse, ka tsaya a nan, zan ba ka allunan dutsen, da doka da umarnan da na rubuta don koyonsu.”

  2. Sa’ad da Ubangiji ya gama yin wa Musa magana a kan Dutsen Sinai, sai ya ba shi alluna biyu na Alkawari, allunan duwatsu rubutattu da yatsan Allah.

  3. Ubangiji ya ce wa Musa “Sassaƙa alluna biyu kamar na farko, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa.

  4. Ka shirya da safe, ka hauro kan Dutsen Sinai. Ka gabatar da kanka a gare ni a can kan dutse.

  5. Ba wani da zai zo tare da kai, ko a gan shi ko’ina a kan dutsen, kada garkunan tumaki ko na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”

  6. Saboda haka Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na fari, sai ya hau Dutsen Sinai da sassafe, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, yana kuma ɗauke da alluna biyu na dutse a hannuwansa.

  7. Ya furta alkawarinsa gare ku, Dokoki Goma, waɗanda ya umarce ku ku bi, ya kuma rubuta su a alluna biyu.

  8. Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya furta da babbar murya ga taronku gaba ɗaya, a can dutse ta tsakiyar wuta, girgije da kuma baƙin duhu; bai kuma ƙara kome ba. Sa’an nan ya rubuta su a kan alluna biyu na dutse, ya kuma ba ni su.

  9. Sa’ad da na hau kan dutse don in karɓi allunan dutse, allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutse yini arba’in da dare arba’in; ban ci abinci ba, ban sha ruwa ba.

  10. Ubangiji ya ba ni alluna biyu wanda shi kansa ya yi rubutu da yatsarsa. A kansu akwai dukan umarnan Ubangiji da an furta muku a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar taron jama’a.

  11. A ƙarshen yini arba’in da dare arba’in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, allunan alkawari.

  12. A lokacin Ubangiji ya ce mini, “Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka haura wurina a kan dutse. Ka kuma yi akwatin katako.

  13. Ni kuwa zan yi rubutu a kan allunan nan biyu, kalmomin da suke a alluna na farko, waɗanda ka farfashe. Za a ajiye su a cikin akwatin.”

  14. Sai na yi akwatin da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, sai na haura dutse da alluna biyun a hannuwana.