Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Stones

79 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa.

  2. Ya kira wannan wuri Betel ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne.

  3. Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa,

  4. har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji zai zama Allahna

  5. kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”

  6. Saboda haka Yaƙub ya ɗauki dutse ya kafa yă zama al’amudi.

  7. Ya ce wa danginsa. “Ku tattara waɗansu duwatsu.” Sai suka kwashe duwatsu suka tsiba, suka kuwa ci abinci a can kusa da tsibin.

  8. Laban ya sa masa suna Yegar Sahaduta, Yaƙub kuwa ya kira shi Galeyed.

  9. Laban ya ce, “Wannan tsibi, shi ne shaida tsakaninka da ni a yau.” Shi ya sa aka kira shi Galeyed.

  10. Aka kuma kira shi Mizfa, domin ya ce, “Ubangiji yă sa ido tsakanin ni da kai sa’ad da muka rabu da juna.

  11. Laban ya ce in ka wulaƙanta ’ya’yana mata, ko ka auri waɗansu mata ban da ’ya’yana mata, ko da yake babu wani da yake tare da mu, ka tuna cewa Allah shi ne shaida tsakaninka da ni.”

  12. Laban ya kuma ce wa Yaƙub, “Ga wannan tsibi, ga kuma wannan al’amudin da na kafa tsakaninka da ni.

  13. Wannan tsibin shi ne shaida, wannan al’amudi kuma shaida ne, cewa ba zan tsallake wannan tsibi zuwa gefenka don in cuce ka ba, kai kuma ba za ka tsallake wannan tsibi da al’amudi zuwa gefena don ka cuce ni ba.

  14. Ubangiji ya ce wa Musa, “Hauro wurina a kan dutse, ka tsaya a nan, zan ba ka allunan dutsen, da doka da umarnan da na rubuta don koyonsu.”

  15. Sa’ad da Ubangiji ya gama yin wa Musa magana a kan Dutsen Sinai, sai ya ba shi alluna biyu na Alkawari, allunan duwatsu rubutattu da yatsan Allah.

  16. Ubangiji ya ce wa Musa “Sassaƙa alluna biyu kamar na farko, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa.

  17. Ka shirya da safe, ka hauro kan Dutsen Sinai. Ka gabatar da kanka a gare ni a can kan dutse.

  18. Ba wani da zai zo tare da kai, ko a gan shi ko’ina a kan dutsen, kada garkunan tumaki ko na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”

  19. Saboda haka Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na fari, sai ya hau Dutsen Sinai da sassafe, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, yana kuma ɗauke da alluna biyu na dutse a hannuwansa.

  20. Ya furta alkawarinsa gare ku, Dokoki Goma, waɗanda ya umarce ku ku bi, ya kuma rubuta su a alluna biyu.

  21. A can za ku bauta wa allolin da mutum ya yi, na itace da dutse da ba sa gani, ba sa ji, ba sa ci, ba kuma iya sansanawa.

  22. Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya furta da babbar murya ga taronku gaba ɗaya, a can dutse ta tsakiyar wuta, girgije da kuma baƙin duhu; bai kuma ƙara kome ba. Sa’an nan ya rubuta su a kan alluna biyu na dutse, ya kuma ba ni su.

  23. Sa’ad da na hau kan dutse don in karɓi allunan dutse, allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutse yini arba’in da dare arba’in; ban ci abinci ba, ban sha ruwa ba.

  24. Ubangiji ya ba ni alluna biyu wanda shi kansa ya yi rubutu da yatsarsa. A kansu akwai dukan umarnan Ubangiji da an furta muku a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar taron jama’a.

  25. A ƙarshen yini arba’in da dare arba’in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, allunan alkawari.