Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome.

  2. Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance.

  3. Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu.

  4. ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’

  5. “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa.

  6. A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba.

  7. Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.”

  8. Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna.

  9. Sa’ad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa, “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa.

  10. Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka.

  11. Amma don kada in ƙara gajiyar da kai, ina roƙonka ka yi haƙuri ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.

  12. “Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa

  13. har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi.

  14. But the chief captain Lysias came upon us, and with great violence took him away out of our hands,

  15. Ta wurin bincika shi da kanka za ka gane gaskiyar game da dukan waɗannan zargin da muke kawo a kansa.”

  16. Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna tabbatar cewa waɗannan abubuwa haka suke.

  17. Da gwamna ya yi masa alama yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina.

  18. Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba.

  19. Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina tā da hankalin jama’a a majami’u ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba.

  20. Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba.

  21. Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa,

  22. ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka.

  23. Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.

  24. “Bayan ’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka.

  25. Ni tsarkake ne sa’ad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina tā da hankali ba.