Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Resignation

132 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wautar mutum kan lalatar da ransa, duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi.

  2. Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka yi tana da kyau.” Gama ya yi tunani a ransa cewa, “Salama da kāriya za su kasance a zamanina.”

  3. Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini! Raunina ba mai warkewa ba ne! Duk da haka na ce wa kaina, “Wannan ciwona ne, dole kuma in jure da shi.”

  4. Ku waɗanda kuka tsere wa takobi, ku gudu kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a ƙasa mai nesa, ku kuma yi ta tunani a kan Urushalima.”

  5. “Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta.

  6. Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?

  7. Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba.

  8. Ku saurara! Ubangiji yana kira ga birni, a ji tsoron sunana kuwa hikima ce, “Ku kasa kunne ga sandan nan da kuma wannan wanda ya naɗa.

  9. Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da ’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa.

  10. mulkinka yă zo a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a sama.

  11. Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”

  12. Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba?

  13. Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

  14. Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”

  15. Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci.

  16. Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi addu’a sau na uku, yana maimaita iri abu guda.

  17. Ya ce, “Ya Abba,Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”

  18. Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce, “ ‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo.

  19. Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.

  20. “Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.”

  21. Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi?

  22. Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”

  23. “Yanzu kuwa na damu, amma me zan ce? ‘Uba, ka cece ni daga wannan sa’a’? A’a, ai, saboda wannan dalili ne musamman na zo.

  24. Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”

  25. Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”