Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Perseverance

159 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.

  2. Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  3. Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.

  4. To, ’yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai.

  5. Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da wa’azin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan.

  6. Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.

  7. Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.

  8. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,

  9. ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.

  10. Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan.

  11. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.

  12. Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.

  13. Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne.

  14. Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.

  15. An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya.

  16. Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.

  17. A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.

  18. da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.

  19. Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara

  20. Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.

  21. Saboda haka ’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!

  22. Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah.

  23. A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku.

  24. Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.

  25. Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.