Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Perseverance: General references

148 ayoyi · 26 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.

  2. Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu, waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.

  3. ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.

  4. Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka.

  5. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.

  6. Ubangiji zai cika manufarsa a kaina; ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada, kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.

  7. Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka.

  8. Zan yi madawwamin alkawari da su. Ba zan taɓa barin aikata musu alheri ba, zan kuma iza su su ji tsorona, don kada su ƙara juya daga gare ni.

  9. Amma dole ku koma ga Allahnku; ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya, ku kuma saurari Allahnku kullum.

  10. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.

  11. amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

  12. “Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa.

  13. Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su.

  14. Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi.

  15. Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa.

  16. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba.

  17. Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.”

  18. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

  19. Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”

  20. “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe kakamar alkama.

  21. Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”

  22. Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.

  23. Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.

  24. Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”

  25. Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.